Yayin da Najeriya Ke Tangal Tangal, Tinubu Zai Sake Karbo Bashin $2.25bn

Yayin da Najeriya Ke Tangal Tangal, Tinubu Zai Sake Karbo Bashin $2.25bn

  • Yayin da Najeriya ke fama da tulin matsaloli, Shugaban kasa, Bola Tinubu zai sake karbo sabon bashin daloli gaba Bankin Duniya
  • Tinubu ya shirya karbo sabon bashin ne har $2.24bn domin tabbatar da inganta tattalin arzikin kasar da yake tangal-tangal
  • Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun shi ya tabbayar da haka inda ya ce kasar ta tsallake dukkan matakan samun bashin a watan Yuli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya karbar sabon bashi daga Bankin Duniya a watan Yuni.

Bola Tinubu zai karbi akalla bashin $2.2bn a ranar 13 ga watan Yunin 2024 da zamu shiga domin inganta tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya, ya dakakar da tsarin biyan harajin 0.5% da CBN ya kawo

Tinubu zai sake karbo bashin makudan kudi daga Bankin Duniya
Bola Tinubu ya amince da karbo bashin $2.25bn daga Bankin Duniya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Ayyukan da Tinubu zai yi da kuɗin

Daga cikin ayyukan da za a yi akwai inganta tattalin arziki wanda zai laƙume $1.5bn da sauran bangarori, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan kuɗi, Wale Edun shi ya tabbatar da hakan inda ya ce bankin Duniya ya tabbatar da cewa Najeriya ta tsallake matakan samun bashin.

Edun ya ce bashin zai kunshi kudin ruwa 1% wanda zai dauki tsawon shekaru 10 kafin fara biyan bashi, Nairametrics ta tattaro.

"Mun samu daman karban bashin $2.25bn daga Bankin Duniya wanda zai kai shekaru 10 kafin fara biya kan kudin ruwa 1%."

- Wale Edun

Bankin Duniya ya soki tsare-tsaren Tinubu

Har ila yau, Bankin Duniya ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na raba tallafi na musamman na N5000 ga talakawa da cewa bai yi amfanin komai ba.

Bankin ya wallafa haka a cikin wani rahoto inda ya ce shirin bai yi wani tasiri wajen rage rashin aikin yi musamman tsakanin mata a kasar nan ba.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

IMF ta koka kan tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar ba da lamuni ta IMF ta nuna damuwa kan dawo da tallafin mai a boye a Najeriya.

Hukumar ta koka kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin dawo da tallafin a sirrance wanda zai jawo asarar makudan kudi.

IMF ta ce akalla Najeriya za ta yi asarar miliyoyin daloli daga cikin kudin shiga na mai da ake tsamanin samu a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel