Bola Tinubu Ya Share Hawayen Iyalan Sojojin da Su ka Mutu, Za a Fito da Hakkokinsu

Bola Tinubu Ya Share Hawayen Iyalan Sojojin da Su ka Mutu, Za a Fito da Hakkokinsu

  • Sojoji da-dama sun mutu wajen kare martabar Najeriya, har yau ba a fitar da hakkokinsu ba
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni da a biya Magadan sojojin da su ka mutu kudinsu
  • Janar Taoreed Lagbaja ya sanar da haka a wajen taro a matsayinsa na shugaban hafsun sojojin kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni da a biya duk wasu hakkokin inshorar rayuwa ga dangogin sojojin da su ka rasu a fagen fama.

Rahoton da aka samu daga Tribune ya ce shugaban hafsun sojojin kasa, Laftanan Janar Taoreed Lagbaja, ya sanar da haka a ranar Talatar nan.

Janar Taoreed Lagbaja ya yi jawabi da yake kaddamar da taron karawa juna sani da sojojin kasa su ka shirya a hedikwatar tsaro da ta ke Abuja.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

Bola Tinubu
Shugaban kasa da hafsun sojoji Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sojoji za su magance rashin tsaro

Hafsun sojojin ya sanar da cewa umarni ya zo daga Bola Ahmed Tinubu da a kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita cikin gaggawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto Lagbaja ya na bayanin yadda gwamnatin tarayya ta samar da wani tsarin inshoran rayukan soji na Group Life Assurance a kasar nan.

Inshoran sojoji bai aiki kenan?

Sojan ya ce gwamnatin Najeriya ce ta ke ware kudi da yawa, ta na biyan kamfanonin inshora wanda za a biya iyalan sojoji idan su ka rasu a yaki.

Duk lokacin da wani soja ya mutu, kamfanin za su biya hakkokinsa ga ‘yanuwan da ya bari.

Jaridar The Sun ta ce ana fama da cikas a gidan soja domin akwai hakkokin sojoji da su ka mutu tun daga 2012 zuwa 2022 da ba a iya biya ba tukun.

Kara karanta wannan

An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama Da Shugaban UAE

Lagbaja ya nuna kamfanonin inshoran ne ba su biyan wadannan kudi, saboda haka gwamnatin tarayya ta dauki nauyin sauke hakkokin da kan ta.

Shugaban kasa ya sa baki, ya bukaci a sallami ‘yanuwa da Magadan wadanda aka rasa a gidan soja.

A wajen taron ne shugaban sojojin kasan ya yi bayanin yadda aka kafa wasu dakaru na musamman domin su tunkari matslolin tsaron da ake fuskanta.

Emmerson Mnangagwa: Kwamacala a Afrika

Ana da labari cewa a Zimbabwe, Shugaban kasar ya sanar da ministoci, ‘dan da ya haifa da wata mata da mijinta sun samu mukami a gwamnatinsa.

Emmerson Mnangagwa ya lashe zabe, ya zarce a kan mulki. Masana su na ganin irin haka ya ke jawo sojoji su kifar da gwamnatin farar hula a Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng