Shugaban kasa Ya Ba Yaron Cikinsa da Wani ‘Danuwansa Kujerun Ministoci a Zimbabwe

Shugaban kasa Ya Ba Yaron Cikinsa da Wani ‘Danuwansa Kujerun Ministoci a Zimbabwe

  • Shugaba Emmerson Mnangagwa ya nada ministocinsa, wadanda aka ba mukaman ya jawo surutu
  • Yaron da shugaban kasar ya haifa, David Kudakwashe Mnangagwa ya na cikin sababbin ministoci a yau
  • Wani daga cikin ‘Yanuwan David Mnangagwa wanda yake majalisar tarayya ya samu kujerar minista

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zimbabwe - Ana ganin wani irin salon shugabanci a nahiyar Afrika, yanzu haka Emmerson Mnangagwa ya nada yaronsa a cikin ministocinsa.

Rahoton da aka samu daga ABC News ya tabbatar da cewa David Kudakwashe Mnangagwa ya zama sabon karamin ministan harkar kudi a Zimbabwe.

Hakan ya na zuwa ne bayan Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben tazarce da aka yi.

Shugaban kasar Zimbabwe
Yaron Shugaban kasar Zimbabwe ya zama Minista Hoto: apnews.com
Asali: UGC

Wannan nadin mukami ya jawowa shugaban kasar mai shekaru 80 suka daga cikin gida har da ketare, ana zargin shi da son kai wajen tafiyar da mulki.

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Minista yaron shugaban kasar Zimbabwe

David Mnangagwa mai shekara 34 a duniya zai zama mataimakin masanin tattalin arzikin nan, Dr. Mthuli Ncube wanda shi zai rike ministan harkar kudi.

Ncube wanda ya ke rike da mukamin nan tun 2018 ya yi karatu a jami’ar Cambridge, sannan ya yi aiki a manyan wurare irinsu bankin AfDB kafin yanzu.

...Tongai Mafidhi Mnangagwa

Baya ga David Mnangagwa, shugaban na Zimbabwe ya zabi yaron ‘danuwansa, Tongai Mafidhi Mnangagwa, ya nada sa cikin ministocin gwamnati.

Legit ta na da labari Mista Tongai Mafidhi Mnangagwa mai shekara 45 ‘dan majalisa ne yanzu haka, zai zama karamin ministan yawon bude ido a kasar.

‘Danuwan shugaban kasar ya na wakiltar mazabar Hunyani a majalisa a jam’iyyar ZANU-PF.

Mata da miji sun zama Ministoci?

AP News ta ce ministoci 26 aka nada a Zimbabwe da ke kudancin nahiyar Afrika. Ana zargin gwamnati mai-ci da sata, rashin gaskiya da rashin kwarewa.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Daga cikin zargin da ake yi wa shugaba Mnangagwa shi ne ya dauko mata da miji; Christopher and Monica Mutsvangwa duk ya ba su kujerar ministoci.

An daure na kusa da shugaban Najeriya

Rahoto ya fito cewa George Turnah wanda yaron siyasar Goodluck Jonathan ne zai shafe shekaru a kurkuku a sakamakon galabaar da EFCC ta yi a kan shi.

Kotun tarayya da ke Fatakwal ta ba hukumar EFCC gaskiya a wata shari’ar satar N2, 894, 500, 000, a dalilin haka aka daure sa a gidan yari tare da wasu mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng