Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

  • Akalla fasinjoji 30 ne aka sanar da mutuwarsu yayin da mummunan hatsarin kwale-kwale ya afku a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja
  • A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba
  • An tattaro cewa 27 daga cikin mamatan mata ne, yayin da uku suka kasance yara

Mokwa, Niger - Rahotannin baya-bayan nan kan hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Neja ya tabbatar da cewar adadin mutanen da suka mutu ya tashi daga 26 zuwa 30.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Hussain Ibrahim, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja (NSEMA) ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba.

Mutum 30 ne suka mutu a hatsarin kwale-kwale
Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, Inji NSEMA Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ibrahim ya tabbatar da cewar yawancin fasinjojin da suka shiga kwale-kwalen mata ne. Da yake ba da rabe-raben wadanda abun ya ritsa da su, ya ce hatsarin ya hada da yara maza uku da mata 27.

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

Ya ce matan na a hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da lamarin ya afku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garuruwa biyar hatsarin kwale-kwale ya shafa, NSEMA

A cewar Hussain, garuruwan da abun ya shafa sun hada da Biagi, Yankyade, Mokwa, Ekwa da Gbajibo.

Ya bayyana cewa har yanzu mutanen da aka ceto suna cikin kaduwa sakamakon faruwar lamarin kuma har yanzu basu yi jawabi sosai a kai ba lokacin da suka isa wajen a ranar Litinin.

A kalla fasinjoji 100 ne aka rahoto cewa suna cikin kwale-kwalen kafin ya yi hatsari da kashe fasinjoji 30.

Hussain ya kuma tabbatar da cewar an ceto fasinjoji 30 amma bai bayyana sunayensu ba.

Mutum 16 yan gida daya sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Neja

A wani labarin, mun ji cewa an tsamo karin gawarwakin manoma shida da suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a garin Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekaru 19 Da Ya Binne Kaninsa Da Rai a Wata Jihar Arewa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutum 16 daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin yan gida daya ne.

Wata cikin dangin da abun ya shafa mai suna Hajiya Kashi Mokwa, ta fada ma jaridar Daily Trust cewa cikin mamatan akwai diyarta, jikoki da sauran yan uwansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng