Kotu Ta Yi Watsi da Karar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar Sanatan APC a Jihar Legas

Kotu Ta Yi Watsi da Karar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar Sanatan APC a Jihar Legas

  • An yanke hukunci kan karar da aka shigar ta neman tsige sanatan wani yankin birnin Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Bayan zaben da aka gudanar a Najeriya, ‘yan takara da yawa ne suka bayyana rashin jin dadi, inda suka tafi kotu neman kadunsu
  • Ya zuwa yanzu, an yanke hukunci a kotun sauraran kararrakin zabe cewa, Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Asabar ta tabbatar da Wasiu Eshinlokun-Sanni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Legas ta tsakiya.

Dan takarar jam’iyyar PDP Francis Gomez, ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Joseph Daudu (SAN), ya koka kan wasu abubuwan yace jam’iyyar APC da dan takararta ba su samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Kawaye sun lakadawa wata mata duka kan wawashe kudi a wurin biki

Ya yi zargin cewa zaben ya kasance dauke da kura-kurai da cin hanci da rashawa, inda ya nemi kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

An tabbatar da zaben dan APC a sanata a Legas
APC ta lashe zabe, an tabbatar da hakan a kotu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai, kotun a wani mataki na bai daya da wasu alkalai uku suka zauna, sun yi watsi da karar da dan takarar na PDP ya shigar, inda suka ce karar ba ta da wani inganci, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hukuncin kotun kararrakin zabe ya kasance

Ba sabon abu bane a Najeriya a samu lokacin da aka yanke hukuncin da bai yiwa wanda ya shigar da kara dadi ba.

A makon da ya gabata ne aka gudanar zaman karshe na kotun sauraran kararrakin zabe, inda aka tabbatar da shugaba Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakan ya jawo cece-kuce daga sauran ‘yan takarar da suka shigar da kara, musamman jam’iyyun PDP da Labour da ke kan gaba, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Sanatan PDP a Kaduna

An tsige sanata a kujerarsa

A wani labarin kuma, kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya mai zama a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ta yanke hukunci kan zaben Sanatan Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Kotun ta ayyana Sanata Gabriel Suswam na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Haka zalika Ƙotun ta tsige Sanata Emmanuel Udende na jam'iyyar APC daga kujerar mamba a majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel