Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

  • Kwanaki kadan su ka ragewa Muhammadu Buhari a ofis, amma ana cigaba da bada kwangiloli
  • Babatunde Fashola SAN ya tunawa masu irin maganar nan cewa su na da ragowar ‘yan kwanaki a ofis
  • Ministan ayyuka da gidaje ya kaddamar da shirin fadada titin Akure zuwaAdo-Ekiti da zai ci N90bn

Ondo - Gwamnatin tarayya ta samu lokaci ta maida martani ga masu sukarta saboda Muhammadu Buhari yana cigaba da bada kwangiloli har gobe.

A rahoton da aka samu daga Vanguard a ranar Juma’a, an ji Babatunde Fashola ya na cewa sai daren ranar mika mulki ne gwamnati za ta daina aiki.

Babatunde Fashola ya ce daga nan har tsakiyar daren 29 ga watan Mayun 20223, gwamnatin Buhari za ta bada kwangila ko ta karbo bashin kudi.

Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ofis Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ministan ayyuka da gidaje na kasar ya yi wannan bayani ne a garin Akure da ke jihar Ondo wajen kaddamar da shirin fara aikin titin Akure/Ado-Ekiti.

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kona Gidan da Ganduje Zai Zauna Bayan Ya Bar Fadar Gwamnatin Kano

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Titin Akure/Ado-Ekiti

The Nation ta ce aikin fadada titin mai kilomita 49 zai ci wa gwamnatin tarayya N90bn, za a kara girman hanyar ne a maimakon a sake gyara ta.

Da yake magana ne sai Ministan yake bada amsa ga masu kokawa a kan yadda gwamnati mai barin-gado ta ke cigaba da bada kwangiloli har yau.

Tunde Fashola ya ce kamfanin NNPCL za su biya kudin aikin a karkashin tsarin haraji da aka fito da shi, ya fadi dalilin da aka gagara aikin da wuri.

Kamfanonin da za su yi aikin su ne Samchase Nigeria Ltd. da Kopeck Construction, ana sa ran a kammala komai a nan da shekaru biyu masu zuwa.

Jawabin Ministan ayyuka da gidaje

"Shiriritar yara ce kurum. Sun manta sai tsakar daren 28 ga watan Mayu ne wa’adin wannan gwamnatin tarayya zai kare.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Titin nan ya nuna yadda abubuwa suka tabarbare a gwamnati daga tituna har zuwa bashin da ake bin gwamnatin Najeriya.
Ana fadan abubuwa iri-iri a game da ni, amma babu abin da ya dame ni, sai dai kara mani karfin gwiwar yin aiki na da kyau.
An yi ta yada karyayyaki cewa Fashola bai kaunar Jihohin Ekiti da Ondo, wannan shirme ne kurum." - Tunde Fashola.

Kwankwaso a Kaduna

A karo na biyu a cikin kwanaki biyu, an ji labari Gwamnan APC ya gayyato jagoran adawa a siyasar Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jiharsa.

Kafin Nasir El-Rufai ya bar mulki, tsohon Gwamnan Kano zai kaddamar da ayyukan da ya yi, a yau zai bude wasu tituna da kuma kasuwa a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel