Yara 35 Nake Sha'awa Kuma Na So Kara Mata 3 Inji Wanda Ya Auri Mata 3 a Rana 1

Yara 35 Nake Sha'awa Kuma Na So Kara Mata 3 Inji Wanda Ya Auri Mata 3 a Rana 1

  • A rana guda kuma a lokaci daya Tersugh Aondona ya angwance da mata uku da ya auro daga garuruwa dabam-dabam
  • Duk da ya angwance da mata da yawa, wannan bawan Allah yayi harin karo amare 3 kafin ya hakura da wannan buri
  • Tersugh Aondona yana so ya tara iyali kuma a samu Farfesoshi, malaman addini, lauyoyi da jami’an tsaro cikin gidansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Benue – A shekarar nan sunan Tersugh Aondona ya yi ta yawo a gidajen jaridu a dalilin auren mata uku da ya yi a jihar Benuwai.

Labarin Tersugh Aondona ya fito a jaridar Guardian, ya auri Blessing, Nancy da Sulumshima kuma aka yi biki a garin Jato-Aka.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala ta kunno kai a gidajen mai a birnin tarayya Abuja, kamfanin NNPCL ya yi magana

Tersugh Aondona
Tersugh Aondona da ya auri mata 3 Hoto: @LisaNwabia/www.gistreel.com
Asali: Twitter

Ba a saba jin wadanda ba musulmai ba sun auri mata fiye da guda musamman a lokaci guda kamar yadda Tersugh Aondona ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tersugh Aondona zai auri mata 6?

A wata doguwar hira da Punch tayi da shi, sabon angon ya bayyana cewa da farko ya yi niyyar ya karo mata uku, matansa su zama shida.

Amma bayan zama da ya yi da matan nasa, sun roke shi cewa ya hakura da batun yi masu kishiyoyi, za su yi masa duk abin da yake so.

"Mun cin ma matsaya da su kuma nayi watsi da shirin."
"Sun kasance suna taimaka mani a gona, kuma suna bin umarnina babu gardama, saboda haka ban da niyyar kara aure."

- Tersugh Aondona

Yara nawa Tersugh Aondona yake so?

Da aka tambaye shi ko ‘ya ‘ya nawa yake so a rayuwa, Tersugh Aondona ya ce 35, kuma yana so a samu kowane irin ma’aikaci a iyalinsa.

Kara karanta wannan

"Za su illata ni": Matashi ya koka da 'yan Nepa suka bar lantarkin tsawon kwanaki 5 a jere

"Idan na samu yara 35, zan gamsu. Ina so in samu yara a bangarori dabam-dabam,"
"Daga ciki a samu lauyoyi, likitoci, fastoci, sojoji, ‘yan sanda, manoma da sauransu."

- Tersugh Aondona

Rikon mata 3 a gidan aure

Duk da kuncin rayuwa da ake ciki, magidancin ya nuna bai shan wahala wajen ciyar da wadannan mata kuma ya ce ba a rikici a gidan.

A cikin matan akwai ‘yar shekara 21 daga Taraba, mai shekara 21 daga Benuwai sai amayarsu da ke shekara 23 da ya auro daga Gboko.

Ana neman Odoh Eric Ocheme

Rahoto ya zo cewa ana tunanin Odoh Eric Ocheme ne ya taimaka aka yi awon gaba da $6.2m daga asusun CBN lokacin Godwin Emefiele.

Wannan mutumi da ake nema yau yana cikin na kusa da Godwin Emefiele. Ana cigiyar Ocheme da matar tsohon gwamnan ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel