Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Rufe Wasu Kasuwanni a Kananan Hukumomi 5 Saboda Matsalar Tsaro

Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Rufe Wasu Kasuwanni a Kananan Hukumomi 5 Saboda Matsalar Tsaro

  • Gwamnatin Zamfara ta rufe wasu kasuwannin dabbobi a ƙananan hukumomi biyar na jihar
  • Hakan ya biyo bayan sayar da shanu da sauran dabbobi na sata da gwamnatin ta ce ana yi a cikinsu
  • Gwamnatin ta kuma bai wa jami'an tsaro da sauran hukumomi na jihar umarnin tabbatar da matakin da ta dauka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gusau, jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara, ta sanar da rufe kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi biyar na jihar sakamakon matsalar tsaro.

Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Zamfara, Mannir Mu’azu Haidara ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnatin Zamfara ta rufe wasu kasuwannin dabbobin jiharta
Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin dabbobi a ƙananan hukumomin jihar biyar. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Kasuwannin da gwamnati ta rufe a Zamfara

Kwamishinan ya ce kasuwannin da abinda ya shafa sun haɗa da kasuwannin shanu na Danjibga da Kunchin Kalgo da ke ƙaramar hukumar Tsafe, da kuma Bagege da Wuya da ke ƙaramar hukumar Anka.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Dau Zafi Kan Kisan Masallata a Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakanan akwai kasuwannin Dangulbi da Dansadau da ke a ƙaramar hukumar Maru, sai Dauran a ƙaramar hukumar Zurmi, da kuma Nasarawar Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyim da ke jihar.

Kwamshinan ya ce an ɗauki wannan mataki na rufe kasuwannin shanun ne a zaman da kwamitin tsaro na jihar ya gabatar a ranar Alhamis da ta gabata.

Dalilin rufe kasuwannin dabbobi a jihar Zamfara

Haidara ya bayyana cewa an rufe waɗannan kasuwannin ne saboda lura da yadda ake sayar da dabbobin da ake tunanin waɗanda aka sato ne a hare-haren da ɓarayin dabbobi ke kai wa a sassan jihar.

Ya yi kira ga jami'an tsaro da kuma na cibiyar kula da lafiyar dabbobi na jihar da su tabbatar da cewa an bi wannan umarnin da gwamnatin jihar ta ba da kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tsoron Juyin Mulki Ya Sanya Kungiyar AU Dakatar Da Kasar Gabon Daga Cikin Mambobinta

Kwamitin ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da sanya idanu kan yadda al'amura ke tafiya har zuwa lokacin da za a samu zaman lafiya a faɗin jihar.

Gwamnatin Zamfara ta musanta umarnin sakin matan 'yan bindiga

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi dangane da umarnin da aka ce ta bayar na sakin wasu matan 'yan bindiga da wasu matasa suka kama.

Gwamnatin ta Zamfara ta ce ba ta ma da masaniya kan batun kama matan da aka anyi ballantana har ta ba da umarnin cewa a sake su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel