Gwamnatin Jihar Rivers Ta Garkame Gidan Rediyo da Na Talabijin Na AIT da RayPower

Gwamnatin Jihar Rivers Ta Garkame Gidan Rediyo da Na Talabijin Na AIT da RayPower

  • Gwamnatin jihar Rivers ta garkame gidan rediyon RayPower a jihar bisa wani sabani da ke tsakanin hukumar gudanarwar kamfanin
  • An ce girke wasu motocin rusau a bakin gidan rediyon da ke cikin birnin Fatakwal a jihar da ke Kudancin Najeriya
  • Rahotanni a baya sun bayyana asalin kitmurmurar da ke tsakanin gwamnatin jihar da kuma fitaccen gidan rediyon na Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Rivers ta garkame tare da dakatar da ayyukan gidan talabijin na Africa Independent Television da Raypower FM a birnin Fatakwal, All News ta tattaro.

A cewar wani rahoto a shafin intanet na kafar yada labaran, injiniyoyin sadarwa da gwamnatin jihar ta dauka ne suka datse ayyukan kamfanin a lokacin da suka zo da jami’an tsaro dauke da makamai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Rufe Kasuwanni a Ƙananan Hukumomi 5 Na Jihar, Ta Ba Da Dalili

Hakazalikam an ga yadda aka watsa kai tsaye a gidan talabijin din lokacin da jami’an ke gimtse hanyoyin sadarwar gidan talabijin din.

AIT aka rufe a jihar Rivers
Yadda aka garkame gidan rediyon AIT a jihar Rivers | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Abin da gidan rediyon ke cewa

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Rivers ta tura motocin rusau domin ruguza ginin kafar watsa labarai na DAAR Communications PLC da ke Fatakwal.
“Hukumar gudanarwar Kamfanin ta yi mamaki bayan faruwar lamarin na kwatsam yayin da ake kokarin sasantawa da Gwamnatin Jihar cikin ruwan sanyi amma babu sanarwa hakan ta faru na akwai matukar damuwa.
“Wasu jami’an dan kwangila na kamfanin sadarwa sun shaida wa AIT cewa suna aiki ne bisa umarni daga sama na a fara rusau din a ranar Lahadi duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake.”

Jaridar Punch ta ruwaito a watan Maris cewa, filin da gidan rediyon AIT/RayPower an gina shi ne a wurin da ake kai ruwa rana tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin.

Kara karanta wannan

Dalibai Za Su Dara a Jihar Arewa Yayin da Gwamnansu Ke Shirin Farfado Da Tsarin Biyansu Tallafin Karatu

An taba rufe AIT a baya

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bukaci Daar Communication, mamallakin gidan talabijin da rediyo na AIT/Ray Power, su bar ginin da suke ciki cikin awa 48.

A cewar PM News, an shirya rusa ginin da kafar watsa labaran ta ke ayyukanta a ciki a unguwar Ozuoba a Fatakwal, babban birnin jihar, cikin awa 48.

An bada wannan gargadin ne cikin wata sanarwar tashi mai dauke da sa hannun sakataren ma'aikatar ayyuka na jihar Ribas, Ebere Dennis Emenike, mai dauke da kwanan wata na 21 da watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel