Ana Zargin Yunwa Ta Kashe Dalibi A Makarantar Horas Da 'Yan Sanda A Jihar Kano

Ana Zargin Yunwa Ta Kashe Dalibi A Makarantar Horas Da 'Yan Sanda A Jihar Kano

  • Wani matashi ya rasa ransa a makarantar horas da 'yan sanda da ke Wudil a jihar Kano
  • Dalibin mai suna A.S Jika, ana zargin ya mutu ne saboda rashin isasshen abinci mai gina jiki
  • Daliban sun koka kan yadda hukumar makarantar karkashin jagorancin sabon kwamanda ke hana su isasshen abinci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wani dalibi dan aji daya a makarantar horas da 'yan sanda da ke Wudil a jihar Kano ya rasa ransa a ranar Asabar 2 ga watan Satumba.

Mutuwar dalibin mai suna A.S Jika ya jawo kace-nace ganin yadda yanayin makarantar take na halin yunwa ga dalibai da kuma rashin abinci mai gina jiki.

Dalibi ya rasa ransa kan zargin rashin abinci a Kano
An Bayyana Yadda Dalibi Ya Mutu Kan Zargin Rashin Isasshen Abinci A Kano. Hoto: @PoliceNG.
Asali: Facebook

Meye daliban ke kokawa a Kano?

Mafi yawan daliban na zargin kwamandan makarantar, mataimakin Babban Sifeta, Sadiq Abubakar da badakalar makudan kudade na abincin dalibai, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Dan Ministan Tsaro Ya Angwance Da Galleliyar Budurwa, Bidiyoyin Shagalin Bikin Ya Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jika wanda ya fito daga jihar Adamawa mai shekaru 19 ya rasa ransa yayin da ya fadi a bandaki da safiyar Asabar 2 ga watan Satumba.

Wani daga cikin dalibai da ya bukaci a boye sunansa, ya ce an garzaya da marigayin zuwa asibitin makarantar bayan faduwar tashi.

Ya ce:

"An bar shi babu kulawa da magani saboda rashin ma'aikantan jinya a makarantar har ya ce ga garinku."

Har ila yau, wani dalibi ya ce a kullum layi ake a asibitin makarantar da babu magani da kayan aiki.

Wasu daga cikin daliban sun koka da yanayin makarantar

A cewarsa:

"Tun bayan karbar ragamar makarantar da sabon kwamandan ya yi, ake ciyar damu da mummunan abinci wanda ba ya isa, matashin da ya rasu ko shekaru 20 bai kai ba.
"Dalibai da yawa na faduwa saboda gajiya na yawan horo da ake basu yayin da kuma babu isasshen abinci mai gina jiki."

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekara 20 Ya Kashe Mahaifinsa Don Asirin Neman Abin Duniya, Bayanai Sun Fito

Ya kara da cewa a kullum suna fuskantar barazana daga kwamandan akan zuwa wurin horaswa wanda ya yi tsanani sosai, Platinum Post ta tattaro.

Ya ce an kori dalibai da yawa saboda rashin lafiya, yayin da wasu ke kokartawa da yunwa don kada a koresu a makarantar.

Dan Daba Da Ake Nema Ruwa A Jallo A Kano Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda

A wani labarin, kasurgumin dan daba ya shiga hannu bayan kama shi ya raunata wani dattijo a jihar Kano.

Wanda aka kaman mai suna Sadiq Ahmad da aka fi sani da 'Big Star' ya shiga hannu bayan illata dattijon da almakashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel