Ayiriri: Dan Ministan Tsaro Ya Angwance Da Galleliyar Budurwa, Bidiyoyin Shagalin Bikin Ya Bayyana

Ayiriri: Dan Ministan Tsaro Ya Angwance Da Galleliyar Budurwa, Bidiyoyin Shagalin Bikin Ya Bayyana

  • Garin Kano ta cika ta tumbatsa a wannan mako yayin da dan ministan tsaro, Mohammed Badaru ya angwace da kyakkyawar amaryarsa
  • An daura auren Ahmad Badaru da tsalekiyar amaryarsa Zainab Nasidi a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba
  • An kuma sha shagulgulan biki kama daga kamu, dina, wankar amarya da sauransu inda amarya da ango suka fito shar da su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Ahmad, dan ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru, ya angwance da sahibarsa, Zainab Nasidi, a wani kasaitaccen biki da aka yi a makon nan.

An daura auren Ahmad da Zainab a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, a babban masallacin Juma'a na Isyaka Rabi'u da ke garin Kano.

An sha shagalin bikin dan ministan tsaro da amaryarsa
Ayiriri: Dan Ministan Tsaro Ya Angwance Da Galleliyar Budurwa, Bidiyon Shagalin Bikin Ya Bayyana Hoto: planning.hub
Asali: Instagram

An sha shagulgulan bikin Ahmad Bdaru da Zainab Nasidi

Kara karanta wannan

Halin Yunwa: Dalibi Ya Rasa Ransa Kan Zargin Rashin Wadataccen Abinci Mai Gina Jiki A Wata Makaranta Da Ke Jihar Kano

Daurin auren ya samu halartan manyan yan siyasar kasar kamar su mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, karamain ministan tsaro, Dr Bello Muhammed Matawalle da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gabannin daurin auren, an sha shagulgula iri-iri da suka kama da wankan amarya, kamu da dai sauransu.

Ma'auratan sun fito shar da su yayin da suka yi shigar kasaita wanda ya dace da su. Amaryar ta sha ado ta fito tamkar wata sarauniya.

A wajen kamu, amarya ta sanya rigar saki kalar ruwan hoda yayin da shi kuma ango ya ci dinkin tazarce na dakakkiyar shadda.

Hakazalika, kawayen amarya sun fito shar da su cikin shiga ta anko kalar koriya.

Ga bidiyoyin bikin a kasa:

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Jama'a sun yi martani yayin da dan ministan tsaro ya angwance da amaryarsa

mace_gimbiya ta yi martani:

"Wannan shiga ta amarya yayi tubarakallah..❤️"

bin_abdourl ya ce:

"Jiki Duk kudiii"

__fantamiii_ ta ce:

"Wadannan kalolin ba 'ya'yan momi na bogi bane ❤️"

ummieyphatemerh_gwalabe ta yi martani:

"Masha Allah sunyi kyau "

ameenerhtuu_ ta ce:

"Masha Allah ❤️"

philter_by_zaay ta ce:

"La har da yar gidan gwauna "

mdanraka_ventures:

"Masha Allah dukkan su masu kyau."

juicevillehub.ng:

"Masha Allah!"

lawalaliyu980:

"Iyayen biki."

Ango ya fasa auren amaryarsa yan kwanaki kafin bikinsu

A wani labari na daban, wani ango ya kekyashe kasa ya ce bayan auren amaryarsa yan kwanaki kafin bikinsu.

Aminin ango ne ya kwarmata masa irin rayuwar da amaryar ta yi a lokacin da suke jami'a, inda ya ce tana raba jikinta domin ta samu maki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel