Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano, Abba El-Mustapha Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano, Abba El-Mustapha Rasuwa

  • Allah ya yi wa mahaifiyar shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha rasuwa
  • El-Mustapha ya sanar da labarin rasuwar Gwagwgo a ranar Talata, 29 ga watan Agusta
  • Manyan jaruman Kannywood sun yi alhinin rashin mahaifiyar shugaba kuma abokin aikinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta shiga juyayi da alhini yayin da mahaifiyar shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano kuma babban jarumi, Abba El-Mustapha ta rasu.

El-Mustapha da kansa ne ya sanar da labarin mutuwar mahaifiyar tasa wacce ya kira da Gwagwgo a ranar Talata, 29 ga watan Agusta.

Abba El-Mustapha tare da mahaifiyarsa
Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano, Abba El-Mustapha Rasuwa Hoto: Dimokuradiyya
Asali: UGC

"Na rasa duniyata", Abba El-Mustapha ya yi alhinin rashin mahaifiyarsa

Da yake nuna alhinin wannan babban rashi da ya yi a shafinsa na Instagram, shugaban hukumar tace fina-finan ya bayyana cewa ya rasa duniyarsa.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta, Jam'iyyar APC Ta Kara Dakatar da Jiga-Jigai 26 Kan Manyan Abu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma sha alwashin ci gaba da jimamin wannan rashi da ya yi har zuwa lokacin da zai daina numfashi a doron kasa.

Ya rubuta a shafinsa:

"INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
"Na rasa mahifiyata kuma DUNIYATA(Gwagwgo).
"Ya Allah Ka jikanta ka gafarta mata kurakuranta kasa Aljanna ce makomarta.
"Zan dunga alhinin rashin ki har zuwa ranar da zan shaki numfashin karshe GWAGWGO.
"R.I.J.F ."

Yan Kannywood sun yi martani kan rasuwar mahaifiyar El-Mustapha

saratudaso ta yi martani:

"Allahu Akbar.Allah yajikansa tayi mata Rahma.Alhamdu lillah kun zauna lfy.kun rabu lfy.kullum shi maka Albarka takeyi har lokacin komawarta ga Allah.Kyma Alhamdu lillah taga cigabanka a rayuwa."

zainaabdoulai ta ce:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un Allah ya sa ta a jannatul firdaus Allah . Shakka babu, Allah na karbar abun da yake nasa, kuma abun da ya bayar nasa ne, kuma yana yin abun da ya so a lokacin da ya so. Don haka ka yi hakuri ka ci riba. Allah Ubangiji ya saka maka da alkhairi, sannan ya baka juriya ya kuma gafarta mata. "

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami

real_hafsta__shehu1 ta ce:

"Allah ya jikan ta da Rahma amen ya Rahman."

washafati ta ce:

"Allah ya jikanta da rahma."

falalu_a_dorayi ya ce:

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun.
"Allah ya jikanta yai mata rahma."

adizatou ta yi martani:

"Allah ya jikanta da rahma ."

rikadawa1 ya ce:

"Allah ya jikanta da Rahma ya yafe mata kurakurenta Amin"

ayshatulhumairah ta ce:

"Ubangiji ALLAH Ya Gafarta Mata.
"Allah Yasa Mutuwa Hutu ce a gare ta.
"Allah ya baku hakurin rashin ta ya kyautata Karshen Mu @abbaelmustapha1."

Legit.ng ta tuntubi El-Mustapha don jin karin bayani daga wajensa, amma har zuwa yanzu bai amsa sakon da wakiliyarmu ta aika masa ta soshiyal midiya ba.

Mahaifiyar Shahararren Mawakin Najeriya Wizkid Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labari na daban, mun ji cewa labari mai sosa zuciya ya mamaye masana'antar mawakan Najeriya a yayin da aka rahoto cewa fitaccen mawaki Ayodeji Balogun ya rasa mahaifiyarsa, Jane Dolapo.

A cewar rahoto da fitaccen shafin watsa labarai na Instagram, Goldmyne, mahaifiyar Wizkid, Jane ta rasu a ranar Juma'a, 18 ga watan Agustan 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel