Hukumar DSS Ta Kama Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Obiora

Hukumar DSS Ta Kama Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Obiora

  • Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta kama Kingsley Obiora, mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) mai kula da manufofin tattalin arziki
  • Koda dai rundunar tsaron sirrin bata tabbatar da lamarin ba amma majiyoyi na kusa sun tabbatar da cewa jami’an DSS na ci gaba da tsitsiye Obiora a halin yanzu
  • Kamun Obiora na da alaka da zargin barnar da aka tafka a karkashin Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan CBN

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rahotanni da ke zuwa mana sun ce jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun tsare mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Kingsley Obiora.

Tsare shi da jami'an tsaron suka yi ya jefa babban bankin kasar a cikin fargaba yayin da yawancin ma’aikatan suka rude.

Jami'an DSS sun kama Kingsley Obiora
Hukumar DSS Ta Kama Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Obiora Hoto: The Department of State Services (DSS), Kingsley Obiora
Asali: Facebook

Wata majiya ta tsaro ta tabbatarwa jaridar The Nation batun tsare Obiora a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Yayin da yake tabbatar da kamun nasa, majiyar ta kuma tabbatar da cewa ba shi kadai ne jami'in CBN da ke tsare a hannun DSS ba amma ya ki bayyana sunayen sauran, New Telegraph ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin da ake ciki, kakakin rundunar DSS, Peter Afunanya bai riga ya tabbatar da ci gaban ba.

Sauran abubuwan da ke da nasaba da kamun da ake zargin an yi wa Obiora

Ana ta yadawa cewa Kingsley Obiora yana tsare a hannun hukumar DSS ne bisa umarnin kwamitin bincike na musamman da shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa don binciken mulkin dakataccen gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele.

An yi zargin cewa kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin Jim Obaze na matsawa Obiora don ya tsaya a matsayin shaida a kan dakataccen shugaban babban bankin.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

Kwamitin yana matsawa Obiora, mai ba da shawara a baya, da ya ba da shaida kan Emefiele.

Yayin da hukumomi ke yi wa wasu manyan jami’an bankin tambayoyi, ba a zargin Dr Obiora da zamba ko sata.

Sai dai kuma, majiyoyi sun bayyana cewa kwamitin ya dage cewa ya san fiye da abun da yake fadi game da mulkin Emefiele, koda dai ya ba da hadin kai sosai duk da kokarin da suka yi na kai shi bango.

Dan sanda ya sharbi kuka a bidiyo bayan an sallame shi daga aiki

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya nuno lokacin da wani jami'in dan sanda ke sharban kuka wiwi bayan an sallame shi daga aiki saboda ya aikata ba daidai ba.

Rundunar yan sandan jihar Adamawa, ta gurfanar da wasu jami'anta biyu, Inspekta Ahmed Suleiman da PC Mahmood Muhammed wanda ke aiki da hedkwatar rundunar ta Dumne a dakin shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel