Ba a Gama da Dambarwar Ganduje ba, an Sake Korar Shugaban APC a Zamfara

Ba a Gama da Dambarwar Ganduje ba, an Sake Korar Shugaban APC a Zamfara

  • Ana tsaka da dambarwar shugaban APC, Abdullahi Ganduje, an sake korar shugaban jam'iyyar a jihar Zamfara
  • Shugabannin jam'iyyar a gundumar Galadima da ke birnin Gusau sun dauki matakin ne game da wasu zarge-zarge kan Tukur Danfulani
  • Daga cikin zarge-zargen akwai nuna wariya da rashin iya shugabanci da kuma saba dokokin jam'iyyar a lokuta da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - An kori shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Tukur Danfulani daga muƙaminsa kan rashin iya shugabanci.

Shugabannin jam'iyyar a gundumar Galadima da ke birnin Gusau su suka dauki wannan matakin kan shugaban APC.

Ana tsaka da dambarwar Ganduje, an sake dakatar da shugaban APC a Zamfara
An kori shugaban APC a Zamfara daga mukaminsa, an bukaci Ganduje ya nada sabon. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

Matakin da APC ta dauka a Zamfara

Shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin, Garba Bello da wasu mutane 15 sun dauki matakin ne kan zarge-zarge da ake yi wa Danfulani, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da su": Jigon APC ya magantu kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello da mukarrabansa suna zargin shugaban jam'iyyar da rashin shugabanci nagari da kuma nuna wariya ga mambobinta a jihar.

Har ila yau, ana zarginsa da karkatar da ayyukan jam'iyyar ga wasu mutane wadanda ba 'yan jami'iyyar ba ne, cewar Tribune.

Shugaban matasan jam'iyyar a Galadima, Abuhuraira Ilyasu ya ce 16 daga cikin shugabanni 27 ne suka amince da daukar wannan mataki.

APC ta bukaci nada sabon shugaba

"A madadin shugabannin jam'iyyar APC a Galadima da ke karamar hukumar Gusau muke sanar da tsige shugabanta na jiha, Tukur Danfulani saboda rashin iya shugabanci."
"Muna da jerin sunayen shugabannin jam'iyyar 16 daga cikin 27 da suka sanya hannu domin tabbatar da tsige shugaban jam'iyyar."

- Abuhuraira Ilyasu

Ya bukaci shugabannin jam'iyyar ta kasa su nada sabon mukaddashin shugaban jam'iyyar a jihar Zamfara bayan dakatar da shi da suka yi.

Kara karanta wannan

Abia: Tsohon shugaban majalisa, tsofaffin ciyamomi da ƙusoshi sun fice daga PDP

"Ganduje yana da sauran haske", Lauyan APC

A wani labarin, kun ji cewa Mai ba da shawara ga jami'yyar APC a bangaren shari'a, Abdulkarim Kana ya magantu kan dakatar da Abdullahi Ganduje.

Kana ya ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar (NWC) ne kawai zai iya daukar wannan mataki kan Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce dole a bi dukkan tsare-tsaren jam'iyyar ba tare da saba wata doka ba kafin tabbatar da dakatar da Ganduje daga muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel