Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara

Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara

  • Zakakuran dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mata 43, kananan yara da kuma wani tsoho 1 daga hannun 'yan Boko Haram
  • Dakarun sun kai samame ne tare da hadin kan jami'an hadin guiwa na CJTF a wasu kauyuka na karamar hukumar Bama
  • Sun yi nasarar halaka 'yan ta'addan masu yawa tare da kwace Ak-47 9, harsasai, babura, kekuna tare da shanu daga wurin miyagun

Bama, Borno - 'Yan ta'adda sun gamu da gamonsu a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno yayin da dakarun sojin Najeriya suka ceto mata 43, kananan yara da wani tsoho.

Dakarun sojin Najeriya na bataliya ta 202 sun lallasa 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suka je kakkabar daji a yankin arewa gabas na jihar Borno, PR Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kai mummunan hari Sakatariyar karamar hukumar da gwamna ya fito

Birged ta 21 dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno ta na karkashin kulawar Birgediya Janar Waidi Shayibu, wanda shi ne babban hafsan soja mai bai wa Div 7 umarni na rundunar sojin Najeriya.

Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara
Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bataliyar wacce ta samu jagoran Laftanal Kanal Isaac Indiohwer tare da hadin guiwar jami'an tsaron hadin guiwa sun tsinkayi maboyar 'yan ta'addan da ke kauyukan Mallum Masari da Gabchari, Mantari, Kanari, Markas, Garin da Baban Baba da ke karamar hukumar Bama ta jihar a ranar 7 ga watan Afirilun 2022 kuma sun halaka 'yan ta'addan masu yawa.

Dakarun sojin sun yi nasarar ceto mata 43, kananan yara da kuma wani tsoho guda daya wanda 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su.

Kamar yadda PR Nigeria ta ruwaito, dakarun soji sun yi nasarar kwace bindigogi kirar Ak-47 guda 9, carbn harsasan Ak-47 guda shida, babura masu yawa da kekuna tare da shanu.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun farmaki asibiti da kwalejin mata a jihar Borno

Borno: Dakarun sojin Najeriya sun gano wurin hada bama-bamai a Sambisa

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Desert Sanity sun gano wuraren da ake gudanar da aikin kera bama-bamai a dajin Sambisa dake Borno.

Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar a wata wallafa da ta yi a shafinta na sada zumuntar zamani na Twitter.

"A ci gaba da aikin share fage, rundunar zakakuran sojoji na Operation Desert Sanity a yau sun sake kai samame sansanin Ukuba/Camp Zairo a dajin Sambisa tare da gano wasu bama-bamai na kungiyar BokoHaram/ISWAP," in ji sanarwar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel