Gwamnan Jihar Jigawa Ya Biya Kudin Makarantar Daliban Jihar

Gwamnan Jihar Jigawa Ya Biya Kudin Makarantar Daliban Jihar

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta amince ta tallafawa ɗaliban jihar da ke karatu a makarantun gaba da sakandire da tallafin kuɗi
  • Gwamnatin jihar za ta biya kuɗin makaranta na ɗaliban jihar masu karatu a makarantun gaba da sakandire guda huɗu
  • An amince da fitar da kuɗin ne har N167m a zaman majalisar zartaswar jihar wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya amince da biyan kuɗin makarantar ɗalibai ƴan asalin jihar masu karatu a makarantun gaba da sakandire.

Gwamnan ya amince da biyan kuɗin makarantar ne ga ɗaliban jihar da ke karatu a jami'o'i guda huɗu, a yayin zaman majalisar zartaswar jihar.

Gwamnatin Jigawa za ta biya kudin makarantar dalibai
Gwamnan ya amince a fitar da N167m domin biyan kudin makarantar Hoto: New Jigawa Media Office
Asali: Facebook

Makarantun su ne jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutse (FUD), jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano da ke Wudil (KUST) da jami'ar Maiduguri (UNIMAID).

Kara karanta wannan

"Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Shiga Ruɗani" Atiku Ya Ƙara Bankaɗo Abinda Tinubu Ya Yi a 1999 da 2023

Sanarwar hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai, wasanni, matasa da al'adu na jihar, Sagir Musa Ahmed ya rattaɓawa hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An bayyana kuɗin da za a kashe

A cewar sanarwar za a kashe jimillar kuɗi har N167m domin biyan kuɗin makarantun ɗaliban.

Majalisar ta amince da biyan kuɗin makarantar ne domin taimakawa iyayen ɗalibai marasa ƙarfi su samu su iya biyan kuɗin makarantar ƴaƴansu a dalilin ƙarin kuɗin makaranta da aka yi a jami'o'i.

Haka kuma majalisar ta amince da sauya tsarin yadda ake biyan ƴan asalin jihar kuɗin tallafin karatu ba tare da ɓata lokaci ba, inda za a riƙa biyan kuɗin yanzu a farkon shekarar karatu.

Sanata Barau Ya Bayar Da Tallafi

A wani labarin kuma, Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ba ɗalibai sama da 600 tallafin karatu.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

Sanata Barau ya bayar da tallafin ne ga ɗaliban da ke karatu a jami'ar Bayero (BUK) da ke Kano. A ƙarƙashin tallafin, kowane ɗalibai zai samu tsabar kuɗi waɗanda suka kai N50,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel