Auren Jinsi: ‘Kun Cancanci Abinda Aka Yi Mu Ku,’ Bobrisky Ya Goyi Bayan Kamen 'Yan Luwadi 100 a Delta

Auren Jinsi: ‘Kun Cancanci Abinda Aka Yi Mu Ku,’ Bobrisky Ya Goyi Bayan Kamen 'Yan Luwadi 100 a Delta

  • Dan daudu Idris Bobrisky, ya yi martani kan kamen masu auren jinsi 100 da aka yi a jihar Delta
  • Ya ce su ne suka janyowa kansu kame tunda sun san dokar Najeriya ta haramta hakan
  • Ya ce kamata ya yi a ce sun tafi can wata ƙasar da ta amince da auren jinsi domin gudanar da shagalin na su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shahararren ɗan Daudun nan Idris Okuneye Olanrewaju, wanda aka fi sani da Bobrisky, ya yi martani gameda 'yan luwadin da jami'an tsaro suka kame a jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Bobrisky ya tofa albarkacin bakinsa kan dambarwar ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Instagram, wanda ya sake ɗorawa a shafinsa na Facebook.

Bobrisky ya yi wa 'yan luwadin da aka kama a Delta Allah ya kara
Bobrisky ya ce 'yan luwadi 100 da aka kama a Delta su suka janyowa kansu. Hoto: Bobrisky
Asali: Facebook

Bobrisky ya ce su suka janyowa kansu kame

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja Ya Fadi Ainihin Abinda Ya Sanya Shi Tattaunawa Da 'Yan Bindigar Jiharsa

A cikin rubutun da ya wallafa, Bobrisky ya ce 'yan luwadin su suka janyowa kawunansu kame daga wurin 'yan sanda tunda suna sane da yiwuwar hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bobrisky ya kuma ce bai kamata su shirya bikin luwadin a ƙasar da suka san an haramta duk wani abu mai kama da hakan ba, kamata ya yi su tafi inda suke da 'yanci.

Najeriya dai ya haramta auren jinsi tun a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, kuma an tanaji hukunci mai tsauri kan duk wanda ya yi kunnen ƙashi.

'Yan luwadi 100 aka kama a jihar Delta

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto kan kamen 'yan luwadi mutum 100 da rundunar 'yan sandan jihar Delta ta sanar da cewa ta yi a wani Otal da ke Ekpan.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Tinubu Ya Nemo Hanyar Sauki, Zai Samar Da Sabbin Gidajen Mai 9,000 Madadin Na Fetur, Bayanai Sun Fito

Rundunar 'yan sandan ta ce ta kama mutanen ne a yayin da suke yunƙurin shirya wani gagarumin bikin auren jinsi a tsakaninsu.

Hukumar 'yan sandan ta sha alwashin gurfanar da wadanda aka kama a shafinta na Facebook domin mutane su shaidasu.

'Yan sandan sun sanar da haka ne a wani rubutu da suka wallafa a shafinsu na X a ranar Talata da ta gabata.

Bobrisky ya gargadi talakawan da ke tura ma sa sako

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da fitaccen ɗan daudu Idris Bobrisky ya yi wa talakawan da ke tura ma sa sakon cewa suna sonsa.

Bobrisky ya bayyana cewa ya canja halittarsa ne domin masu kuɗi ba domin talakawa ba, a don haka ya nemi su fita harkarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel