Ban canja suffata domin talakawa ba, na yi don manyan 'yan siyasa ne - Dan daudun da ya canja suffarshi daga namiji zuwa mace

Ban canja suffata domin talakawa ba, na yi don manyan 'yan siyasa ne - Dan daudun da ya canja suffarshi daga namiji zuwa mace

- Fitaccen daudun jihar Legas, Bobrisky ya yiwa talakawa da suke tura masa sakon cewar suna son shi gargadi

- Inda ya bayyana musu cewa shi bai canja siffarsa domin su ba, ya canja siffarsa domin 'yan siyasa ne

- A karshe ya gargade su da su fita harkar shi, domin zai ci musu mutuncin idan basu daina aiko masa da sako ba

Fitaccen dan daudun nan dake zaune a jihar Legas Bobrisky yayi wata magana dan gane da dalilin da yasa ya shiga harkar daudu, wanda yasa ya canja kamaninshi daga namiji zuwa mace, a yau Asabar dinnan.

Dan daudun ya caccaki talakawa, inda ya bayyana cewa bai shiga wannan harkar dan su bane, ya shiga domin manyan 'yan siyasa ne Najeriya da kuma na kasashen ketare. Bobrisky ya bayyana cewa bai canja halittarshi domin talakawa ba, inda yayi musu gargadin su fita harkar shi.

KU KARANTA: A titi muke kwana ni da 'ya'yanmu idan mijina ya kawo karuwa gida har sai sun gama zinar su akan gadon mu na sunnah - Wata mata ta koka

Ga abinda dan daudun ya rubuta:

"Ina so ku sani, duk wadannan matsiyatan da suke turo mini sako cewar suna sona, kada ku bari na ci muku mutunci. Kuna nufin na canja siffata saboda kune? Kyau na saboda manyan 'yan siyasar mu ne na Najeriya da kuma na wasu kasashen, saboda haka ku fita harka ta.

"Matsayina yanzu sai dai nayi harka da manyan masu kudi na duniya."

Bobrisky dai wani dan namiji ne da yake zaune a jihar Legas, wanda yake da musulmi ne amma ya canja addini saboda ya bayyana cewa addinin Musulunci bai kamace shi da wannan harkar tashi ba.

Hakan yasa ya koma addinin Kiristanci yaje aka canja masa siffarsa daga namiji zuwa mace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng