Tirkashi: Direban fitaccen dan luwadin nan Bobrisky ya arce masa da mota da kudi rabin miliyan a ciki

Tirkashi: Direban fitaccen dan luwadin nan Bobrisky ya arce masa da mota da kudi rabin miliyan a ciki

- Bobrisky ya wallafa yadda wani direban shi ya yi awon gaba da motar shi tare da wasu makuden kudade

- Kamar yadda ya ce, ya aika direban gyaran motar ne tare da ba shi wasu kudi don gyara a cikin gida

- A halin yanzu ya kai rahoto wajen 'yan sanda bayan ya kasa samun wayar direban kuma babu motar shi balle kudi

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, Bobrisky ta koka a kafar sada zumuntar zamani yadda direban shi yayi awon gaba da motar shi kirar Mercedes Benz da kuma N600,000.

Mata-mazan ya bayyana yadda ya dinga yafewa direban nashi bayan kama shi da ya dinga yana mishi sata. A yanzu kuwa guduwa yayi da motar da ya bashi don kaiwa wajen gyara.

Bobrisky ya kara da cewa, a halin yanzu dai lambar wayar direban na kashe bayan yayi awon gaba da motar. Amma kuma tuni ya kaiwa 'yan sanda rahoto.

KU KARANTA: Babbar magana: Maza ne suka kirkiro addini kawai dan su dinga zalintar mata - Efia Odo

Kamar yadda ya wallafa tare da hoton direban "wannan shine tsohon direbana. Ya saba yi min sata amma sai ya rokeni a kan in yi hakuri. Akwai lokacin da na koreshi don gudun rigima. A watan da ya gabata ne ya kira ni inda ya rokeni har na dawo da shi. A cewar shi ya canza hali kuma zai dage da aikin shi."

Ya kara da cewa "ubangidanshi ya koreshi a inda ya fara aiki. Ni kuwa halin tausayi da jin kai yasa na dawo da shi bakin aikin shi. A halin yanzu ya kara yi min sata. Mota ta kirar Benz cla 300 na aikeshi ya kai gyara a ofishin Benz da ke Lekki. Tana kara ne wajen tayar farko ta dama. Na bashi N200,000 ya rike ko za a bukaci kudin wani abu ko na gyaran tunda ni tafiya zanyi."

"A ranar kuma na tura mishi N396,000 don wasu aiki da za a yi a cikin gidana. Har yanzu dai naji shiru kuma wayar shi ba ta shiga. Ba mota ta ko kudina wanda ke nuna ya gudu kenan. Dukkan wayoyin shi na kashe. Na kai wa 'yan sanda rahoto a halin yanzu, duk inda yake za a binciko shi." Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: