Yan Sanda Sun Kama Yan Luwadi Sama da 10 Suna Auren Jinsi a Jihar Delta

Yan Sanda Sun Kama Yan Luwadi Sama da 10 Suna Auren Jinsi a Jihar Delta

  • Hukumar 'yan sanda reshen jihar Delta ta sanar da cewa jami'anta sun kama 'yan luwaɗi sama da 100 a wani Otal
  • A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne suna shagalin bikin auren 'yan luwaɗi
  • A zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan aka kafa dokar haramta auren jinsi da luwaɗi a Najeriya

Delta state - Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa ta cafke sama da ‘yan luwadi 100 da ake zargi da shirya bikin auren ‘yan luwadi a wani otal a jihar da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da damƙe 'yan luwaɗin ne a wata sanarwa da ta wallafa shafinta na Tuwita, wanda aka sauya zuwa X ranar Talata, 28 ga watan Agusta, 2023.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Waɗanda ake zargi a jihar Delta.
Yan Sanda Sun Kama Yan Luwadi Sama da 10 Suna Auren Jinsi a Jihar Delta Hoto: Thenation
Asali: UGC

Sanarwan ta ce:

"Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta kama 'yan luwaɗi sama da 100 da ake zargi a Otal suna shagalin bikin auren jinsi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Nan ba da jimawa ba zamu ɗauki bidiyo kai tsaye a shafin Facebook domin nuna waɗanda ake zargin."

Luwadi haramun ne a Najeriya

Dokar hana luwadi a Najeriya, wacce gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kafa a watan Janairun 2014, ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka samu da laifin ƙulla alakar 'yan jinsi daya.

Gwamnatin Najeriya ta gwada dokar a karon farko a watan Disambar 2019 lokacin da 'yan sanda suka kama mutane 47 da zargin luwaɗi a wani otal a Legas.

Hukumar 'yan sanda ta gurfanar da su a gaban Kotu bisa zarginsu da nuna soyayya ƙarara ga yan jinsi ɗaya, wanda hakan ya saɓa wa dokar haramta auren jinsi.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Gwamnan Arewa Ya Lale Kudi Sama da Biliyan Ɗaya Ya Siyo Motoci 10 Domin Taimaka Wa Talakawa

Sai dai baki ɗaya mutane 47 da hukumar 'yan sandan ta gurfanar sun musanta aikata abinda ake tuhumarsu da shi kuma daga bisani Kotu ta bada belinsu.

Daga bisani wani alkali kotun tarayya ya yi fatali da tuhumar da ake yi wa mutanen saboda “rashin gurfanar da su yadda ya kamata" da ‘yan sanda suka yi.

Hukumar Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja

A wani labarin na daban rundunar 'yan sandan jihar Neja ta maida martani kan labarin da yawo cewa wani hatsabibin ɗan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamna.

Kakakin 'yan sandan jihar, Wasi'u Abiodun, ya ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma jami'an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel