Hukumomi A Indiya Sun Rufe Makarantar Da Aka Ci Zarafin Dalibi Musulmi Da Maruka

Hukumomi A Indiya Sun Rufe Makarantar Da Aka Ci Zarafin Dalibi Musulmi Da Maruka

  • Wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa an gano dalibi Musulmi mai shekaru bakwai na tsaye yayin da dalibai ke marinshi daya bayan daya
  • Ana zargin wata malamar makarantar ce ta ke ba su umarni kamar yadda aka gano a cikin faifan bidiyon a Arewacin jihar Uttar Pradesh da ke Indiya
  • Hukumomi a kasar sun rufe makarantar tare da umartar malamar ta gurfana a gabansu don bincike kan tuhumar nuna wariya da cin zarafi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uttar Pradesh, Indiya – Hukumomi a kasar Indiya sun ba da umarnini rufe makaranta a Arewacin jihar Uttar Pradesh bayan cin zarafin dalibi Musulmi.

Ana zargin wata malamar makarantar da ba da umarnin yi wa wani dalibi Musulmi taron dangin maruka.

Indiya ta rufe makarantar da aka ci zarafin dalibi Musulmi
Malamar Kenan Yayin Da Ta Ke Umurtan Daliban Kan Marin Yaron. Hoto: Arab News.
Asali: Facebook

Meye malamar ke yi wa dalibi Musulmi?

A wani faifan bidiyo, an gano wani dalibi mai shekaru bakwai na tsaye inda malamar ta ke umurtan daliban daya bayan daya su ta so suna marinshi.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An jiyo malamar wacce ke bin addinin Hindu kamar yadda CNN ta tattaro na cewa:

“Me kuke yi? Me yasa bakwa dukansa sosai.”

Jami’an ‘yan sanda a ranar Litinin 28 ga watan Agusta sun bukaci ganin mai kafar sadarwa ta Alt News, Mohammad Zubair kan nuna surar yaron da ake mara.

Zubair shi ne ya yada bidiyon a shafinsa na Twitter yayin da 'yan sanda su ka dauki mataki bayan yayata bidiyon.

Wane hukunci aka dauka kan cin zarafin dalibi Musulmi?

Hukumomi sun ce makarantar za ta kasance a kulle har zuwa lokacin da za a kammala bincike, cewar CBS News.

Jami’in ilimi, Shubham Shukla ya bayyana cewa malamar za ta halarci gudanar da binciken kuma gwamnati za ta kwace takardar shaida da ta bai wa makarantar.

Lamarin ya faru ne a kauyen Khubbafur inda mutane da dama daga sassan duniya su ka nuna bacin ransu a kan haka.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

An Rufe Makarantu A Indiya Bayan Rikici Kan Hana Saka Hijabi

A wani labarin, Hukumomi a kudancin Indiya sun bada umurnin rufe makarantu ranar Talata yayinda zanga-zanga ya barke kan hana dalibai mata Musulmai shiga aji da Hijabi.

Rikicin wanda ya barke a jihar Karnataka ya tada hankulan jama'a saboda cin zarafin da yan addinin Hindu ke yiwa Musulmai karkashin mulkin Firai Minista Narenda Modi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel