Bidiyon Jarumar Fim Da Attajirin Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Jarumar Fim Da Attajirin Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

  • Shahararriyar jarumar Nollywood Regina Daniels ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da bidiyonta da biloniyan mijita Ned Nwoko a wajen wani biki ya bayyana
  • Masoya sun garzaya shafin jarumar inda suka dungi jinjina mata kan daukakar da ta samu wanda ya sha banban da na yan fim a Najeriya
  • Ma'auratan sun dauki hankali a wajen bikin da aka yi a Abuja wanda yake na diyar takwaran mijinta ne, Sanata Sani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo na jarumar Nollywood Regina Daniels tare da biloniyan mijinta, Ned Nwoko, a wajen bikin diyar Sanata Sani ya dauka hankali

A cikin bidiyon da ya yadu, Regina ta fito shar da ita inda ta dunga walwali sannan ta kasance dauke da murmushi a fuskarta wanda ya kara fito da tsantsar kyawunta.

Kara karanta wannan

“Tana Biyan 238k Duk Wata”: Yar Najeriya Ta Baje Kolin Dakinta a Kasar Japan, Bidiyon Ya Yadu

Regina Daniels da mijinta Ned Nwoko sun halarci bikin diyar sanata Sani
Bidiyon Jarumar Fim Da Attajirin Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet Hoto: @regina.daniels
Asali: Instagram

Jaruma Regina Daniels cikin manyan matan sanatoci

An gano jarumar tana gaisawa da sauran manyan mata da suka girme mata a wajen taron, sannan ta fito shar tamkar kifi a cikin kogi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba da yanayin shigar Regina. A lokaci guda, wasu sun kwararo ruwan yabo ga jarumar kan daukakar da ta samu daga jarumar fim zuwa wata babbar mutum a cikin al'umma.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon Regina Daniels a wajen bikin diyar Sanata Sani

@zubbyprisca042:

"Regina kadai ce ke cin duniyarta a Najeriyar nan, gaba daya sauranmu za mu dunga bayani har mu gaji ba hujja."

@simeon.delight:

"Daga Regina har Ned duk walwali suke, kwanciyar hankali da kudi suna da kyau."

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

@moonshine_skincareng:

"Lallai kin shirya kuma horar da kanki sosai a wannan tafiyar, karin darajar a halayya, nutsuwa da yadda kike magana duk suna da kyau, sannu da kokari Gina."

@corazon_berry:

"Wahala bata da kyau gaskiya. Yar'uwa, kin yi zabi nagari."

@only_one_milly:

"Shin ku ga wannan?? MATAN SANATAOCI."

@loveaca2018:

"Regina ce kadai ta yi zabi nagari a kasar nan...smh."

Budurwa ta dauki hankali da yanayin rawanta a wajen biki

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa Bahaushiya ta burge masu amfani da soshiyal midiya saboda yanayin rawar da ta yi a wajen wani taro.

A bidiyon da aka wallafa a TikTok wanda ya samu mutum sama da miliyan da suka kalla, an gano matashiyar tana rawa tare da girgiza kwankwasonta yayin da wani kida ke tashi daga kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng