Soyayya Ruwan Zuma: Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Bikinsu Ya Dauka Hankali

Soyayya Ruwan Zuma: Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Bikinsu Ya Dauka Hankali

  • An dauki bidiyon shakuwar da ke tsakanin wata amarya da angonta a lokacin shagalin bikinsu sannan aka yada shi a TikTok
  • Bidiyon ya nuno angon yana bude mayafin da aka lullube fuskar amaryar da shi, kwatsam sai ya ci karo da ita tana kanne masa ido daya da gwalo
  • Sai ma'auratan suka fashe da dariya, suna masu nuna yadda suke nishadantuwa da kasancewarsu tare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An dauki bidiyon wani yanayi mai kayatar da zukata tsakanin wata amarya da angonta a wajen shagalin bikinsu sannan aka yada shi a TikTok, inda daga nan kuma ya yadu.

Bidiyon ya nuno angon yana cire mayafin da ya lullube fuskar amaryar a hankali a yayin budar kai.

Amarya da ango wajen budar kai
Soyayya Ruwan Zuma: Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Bikinsu Ya Dauka Hankali Hoto: @chrisstilldey
Asali: TikTok

Sabbi ma'aurata sun nuna shakuwar da ke tsakaninsu a wani gajeren bidiyo

Yayin da ya ga kyakkyawan fuskarta, sai ta yi masa murmushi mai sanyaya zuciya tare da kanne masa ido daya da kuma gwalo, lamarin da ya sa shi murmusawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya tsuma zukatan mutane da dama a TikTok inda suka bar dubban martani a sashin sharhi tare da jinjinawa shakuwar da ke tsakanin sabbin ma'auratan.

Mutane da dama sun kuma nuna sha'awarsu ga hadaddiyar rigar da amarya ta sanya da kuma kwalliyarta, da kuma babban rigar da hadadden angon ya sanya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@EdmundTetteh197ya yi martani:

"Abun da nake gani a nan shine aure mai dorewa."

@Ameerahyola ta ce:

"Ku kyale marasa aure su numfasa."

@Nr.Jamee ya rubuta:

"Ba wai yan auta ba kawai, idan ka auri aminiyarka ma."

@Shatura101 ta yi martani:

"Menene laifunmu. Abun da zan iya yi. Amarya mai son wasa."

@Blackmelani ma ta yi martani:

"Ku kyale mu haka. Zan rama nawa. Abun da zan iya yi."

@User5234504474799:

"Idan ka mayar da matarka abokiyarka."

Kara karanta wannan

“Karin ‘Da 1 Kacal Na Nema”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ta Haifo Tagwaye, Ta Mika Masa Su a Bidiyo

Matashi ya roki barawon da ya sace masa waya ya tura masa lambar wata tsohuwar kilakinsa

A wani labari na daban, wani mutumi ya baiwa mutane mamaki bayan ya roki barawon da ya sace masa waya da ya taimaka ya tura masa da lambar wata tsohuwar kilakinsa.

A cewar matashin, wannan mata ita ce ke taimakonsa a bangaren kudi ciki harda biya masa kudin hayar gidan da yake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng