Kwamandojin Boko Haram 4 Da Mayaka 13 Sun Mika Wuya Ga Sojoji a Jihar Borno

Kwamandojin Boko Haram 4 Da Mayaka 13 Sun Mika Wuya Ga Sojoji a Jihar Borno

  • Shan ragargaza daga hannun dakarun sojoji ya sanya ƴan ta'addan Boko Haram miƙa wuya a jihar Borno
  • Kwamandoji 4, maƴaka 13 tare da iyalansu 45 ne miƙa wuya a hannun dakarun sojojin bayan sun ji azaba
  • Ƴan ta'addan sun kuma miƙa muggan makamai masu ɗumbin yawa a hannun jami'an tsaron sojojin

Jihar Borno - Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun miƙa wuya ga rundunar dakarun haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a jihar Borno.

Ƴan ta'addan waɗanɗa suka haɗa da kwamandoji 4 da mayaƙa 13 tare da iyalansu 45 ne suka miƙa wuya ga dakarun sojojin.

Yan ta'addan Boko Haram sun mika wuya
Wasu daga cikin wadanda suka mika wuya Hoto: @MNJTFOfficial
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar MNJTF, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne bayan rundunar ta ƙara ƙaimi wajen ragargazarsu.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zaben Shugaban Kasa Kan Yin Hukuncin Da Zai Haifar Da Rikici a Kasa

Ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne a tsakanin ranakun 14 zuwa 15 na watan Agusta, inda suka ajiye makamansu na yaƙi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne ga dakarun rundunar na sashe na uku a tsakanin Kauwa da Baga cikin ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun miƙa makamai masu yawa

Ƴan ta'addan sun kuma miƙa bindigu ƙirar AK-47 guda bakwai, bindiga ɗaya ƙirar SLR da harsasai masu yawa kusan 440 da sauran kayan aikata ta'addanci.

Ya ƙara da cewa sauran kayayyakin da ƴan ta'addan suka miƙa wa jami'an tsaron sun haɗa da bindigu ƙirar AK-47 guda biyu, jigidar harsasai guda bakwai, rediyo guda biyu, harsasai guda 99 masu kaurin 7.6mm da tsabar kuɗi har N213,800.

"A bisa wannan gagarumar nasarar da aka samu, rundunar MNJTF na sake ƙara jaddada kiranta ga ragowar ƴan ta'addan Boko Haram, da su rungumi zaman lafiya su miƙa wuya ta hanyar ajiye makamansu." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Kwamandan Boko Haram Da Ya Jagoranci Kashe Mayaka 82 Ya Mika Wuya

Ya ƙara bayyana cewa rundunar a shirye take wajen ganin ta dawo da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.

Rikicin Kabilanci a Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin ƙabilanci ya ɓarke a tsakanin mayaƙan Boko Haram a dajin Sambisa.

Rikicin wanda ya ɓarke a tsakanin ƙabilun da ke cikin mayaƙan ƙungiyar ya aujuɓne bayan wani kwamandan ƙungiyar ya halaka wasu mayaƙan ƙungiyar waɗanda ba ƴan ƙabilarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel