Jerin Sunaye: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai

Jerin Sunaye: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai

  • Gwamnatin tarayya ta amince da nadin sabbin manyan daraktocin kiwon lafiya 11 a asibitocin tarayya
  • Ma'aikatar lafiya, ta hannun darakta Patricia Deworitshe, ta sanar da nade-naden sannan ta ba da jerin sunayen sabbin daraktocin
  • Kachollom Daju, sakatariyar dindindin na ma'aikatar ce ta gabatarwa wadanda aka nada da takardun nadinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da nadin sabbin daraktocin kiwon lafiya a manyan asibitocin tarayya guda 11.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar ma'aikatar lafiya, Patricia Deworitshe, ta fitar, jarida The Guardian ta rahoto.

Bola Tinubu ya nada daraktocin kiwon lafiya
Jerin Sunaye: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa sabbin daraktocin da aka nada za su yi aiki na tsawon shekaru hudu.

An mayar da nadin nasu baya zuwa kwanan wata Talata, 1 ga watan Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Abubakar Momoh: Tsohon Malamin Sakandare, Tsohon Shugaban SUG, Da Wasu Abubuwa Kan Sabon Ministan Matasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

  1. Nyandanti Yakub Wilberforce, Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya, Hong, jihar Adamawa
  2. Issa Baba Awoye, asibitin kula da lafiyar kwakwalwa na tarayya da ke Buddo-Egba, Kwara
  3. Umar Faruk Abdumajid, Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya, Daura, jihar Katsina
  4. Muhammad Shittu Adamu, Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya, Wase, jihar Filato
  5. Shuaibu Jauro Yahya, Cibiyar Kiwon Lafiya Mubi, jihar Adamawa
  6. Mercy Anugwu, Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya Onitsha, jihar Anambra
  7. Auwalu Sani Salihu, asibitin masu tabin hankali na tarayya da ke Dawanau jihar Kano
  8. Rufai Ahmed, Hukumar Kula da Lafiya ta Najeriya
  9. Mangwa J. Kortar, Cibiyar Kiwon Lafiya, Makurdi, jihar Benue
  10. Robinson Chukwudi Onoh, Alex Ekwueme, asibitin koyarwa ta jami'ar tarayya, Abakiliki, Ebonyi state
  11. Nurudeen Isa, asibitin kashi na kasa, Dala, jihar Kano

An mika wa sabbin daraktocin takardar kama aiki

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

A jawabin da ta gabatar na wasikun nadin nasu, Kachollom Daju, sakatariyar dindindin na ma’aikatar, ta taya sabbin daraktocin da aka nada murna, rahoton The Cable.

Ta kuma karfafa musu gwiwa da su hada kai da ma’aikatan lafiya da masu ruwa da tsaki, tare da gudanar da aiki tare a matsayin kungiyar hadin gwiwa.

Ta nusar da manyan daraktocin muhimmancin samar da ingantaccen yanayin aiki da inganta ababen more rayuwa don samun ingantaccen matakin ingancin kiwon lafiya.

Yan arewa sun nemi a gaggauta tabbatar da El-Rufai a matsayin minista

A wani labarin, mun ji cewa wata kungiya mai suna 'Like Minds Forum of Nigeria', ta soki takkadamar da ke kewaye da nadin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da aka yi a matsayin minista.

Kungiyar ta arewa ta soki majalisar dattawan Najeriya kan kin tabbatar da El-Rufai a matsayin minista, inda ta bayyana hakan a matsayin kuskure da tabarbarewar siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel