Bincike: Shin Da Gaske Shugaban Amurka, Biden Ya Fadi Cewa Buhari Ya Mutu Shekaru 6 Da Suka Wuce?

Bincike: Shin Da Gaske Shugaban Amurka, Biden Ya Fadi Cewa Buhari Ya Mutu Shekaru 6 Da Suka Wuce?

  • Gaskiya ta bayyana bayan ganin shugaban Amurka, Joe Biden na cewa Buhari ya mutu shekaru shida da su ka wuce
  • Masu binciken kwakwaf sun tabbatar da cewa bidiyon da ake yadawa a kafofin yada labarai musamman WhatsApp karya ne
  • A binciken an tabbatar da cewa Joe Biden bai fadi wannan magana ba kuma BBC ba ta kawo rahoto kan Biden ba inda ya ke fadan haka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Bayanai sun fito kan faifan bidiyon da ake yadawa cewa matacce ne ke mulkin Najeriya da kuma cewa tsohon shugaban kasa, Buhari ya mutu shekaru shida da su ka wuce.

Bidiyon mai tsawon dakika 47 ya yadu a manhajar WhatsApp inda shugaban Amurka Joe Biden ke cewa Buhari ya mutu shekaru shida da su ka wuce, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

Bidiyon Biden na cewa Buhari ya mutu shekaru 6 da su ka wuce karya ne
Bayanai Sun Fito Kan Gaskiyar Ko Shugaban Amurka Biden Ya Fadi Cewa Buhari Ya Mutu Shekaru Shida Da Suka Wuce. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

An gano faifan bidiyon a BBC inda ma'akaciyarsu Sophie Raworth ta nuna bidiyon da Biden ke cewa matacce ne ke mulkin Najeriya.

Meye Biden ke cewa a kan mutuwar Buhari?

A faifan bidiyon, an gano Biden na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Najeriya ce kadai kasar da matacce ke mulkinsu na tsawon shekaru shida amma ba su sani ba."

A wani bincike da aka yi da Daily Trust ta tattaro an bayyana cewa bidiyon bai inganta ba.

Meye bincike ya tabbatar kan mutuwar Buhari?

Masu binciken sun tabbatar da haka bayan amfani da manhajar Google don binciken, kuma ya tabbata faifan bidiyon karyane.

Rahoton ya tabbatar cewa babu inda Biden ya fadi haka kuma BBC ba ta dauki wannan rahoto ba.

A martaninsa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa masu fadar Buhari ya mutu su na da tabin kwakwalwa inda ya ce tsananin tsoron Buhari ne ya saka su susucewa.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Ba Mamaki Buhari Ya Mutu, Femi Fani-Kayode

A wani labarin, tsohon minista sufuri Femi Fani-Kayode ya ce babu mamaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mutu ganin ya ake ta boye-boye a fadar shugaban kasar kan yanayin lafiyarsa.

Kayode ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa Daily Post da cewa kumbiya-kumbiya da fadar ke yi ya sa 'yan Najeriya cikin rashin tabbas da kuma son jin ainihin abin da ke faruwa da shugaban nasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel