Babu mamaki ma Buhari ya mutu – Fani-Kayode

Babu mamaki ma Buhari ya mutu – Fani-Kayode

- Femi Fani-Kayode ya ce kila shugaba Muhammadu Buhari ya mutu

- Ya kalubalanci fadar shugaban kasa da ta daina yawo da hankalin jama'a ta filo fili ta bayyana gaskiya a kan halin da yake ciki

- Ya kuma ce a kawo hujja da zai tabbatar da cewa yana nan da ransa bai mutu ba kamar yadda suke ikirari

Tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayose ya ce babu mamaki kila ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu.

Hakan na kunshe ne a cikin sabon labara da ya aika ma jaridar Daily Post a safiyar ranar Juma’a.

Ya ce kunbiya-kunbiya da fadar shugaban kasa keyi ya sa ‘yan Najeriya cikin rashin kwanciyar hankali sannan kuma yasa suka kalubalanci gwamnati da ta saki hotunan shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar IboKalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Babu mamaki ma Buhari ya mutu – Fani-Kayode
Babu mamaki ma Buhari ya mutu inji Fani-Kayode

Tsohon kakakin shugaban kasar y ace: “Fadar shugaban kasa ta bayyana mana cewa Buhari ya yi tafiya zuwa wajen kasar amma har yanzu babu wanda ya hotuna ko sahun sa a lokacin da ya ke barin Najeriya ko kuma lokacin da ya isa kasar wajen da aka ce.

“Misali a ce da gaske ya yi tafiya muna al’ajabin wacce kasa aka kais hi, da kafa ya je ko da bayan sa sannan kuma shin yana a asibiti ne ko kuma yana wani kebantaccen guri ne.

“Fadar shugaban kasar ta yi ikirarin cewa yana raye har yanzu sannan kuma muna sa ran cewa Allah ya sa haka zancen ya ke.

“Babu yarda a tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka a Najeriyarmu ta yau.

“Maganar shine: Idan shugaban kasar ya mutu, a daina wasa da hankulan jama’a, a fada mana gaskiya, a binne shi da daraja sannan a bari ruhinsa ya huta.

“Idan kuma yanba raye a bari mu san ainahin abun da ke damun sa, halin da yake ciki, inda yake, yadda yake, sannan kuma mafi muhimmanci a nuna mana hujjar yana raye’, Inji Fani-Kayode.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng