Tsohon Shugaban Binance, Chanpeng Zhao ya Zama Fursuna Mafi Arziki a Duniya

Tsohon Shugaban Binance, Chanpeng Zhao ya Zama Fursuna Mafi Arziki a Duniya

  • Wata kotu a birnin Seattle da ke Amurka ta daure tsohon shugaban kamfanin Binance Chanpeng Zhao na watanni 4
  • Ana zargin Mista Zhao da ba bata-gari dama su yi amfani da kafar Binance wajen almundahanar kudade masu yawa
  • Chanpeng Zhao ya amsa laifinsa, tare da neman afuwa bayan ya amince da wata yarjejeniya da ma'aikatar harkokin Shari'a ta Amurka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Seattle, US- Tsohon shugaban kamfanin hada-hadar kudade a yanar gizo na Binance, Chanpeng Zhao ya zama fursunan da ya fi kowanne daurarre arziki a duniya.

Kotun da ke zamanta a Amurka ta daure Chanpeng Zhao wanda shi ne ya kirkiro kamfanin Binance na watanni hudu bayan ya amsa laifin da ake tuhamarsa da aikatawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya nemi hadin kan kasashe kan matsalar da ta addabi duniya

Chanpeng Zhao ya nemi afuwa a kotu
An sassauta daurin ne bayan Mista Zhao ya shiga yarjejeniya da ma'aikatar shari'a ta Amurka Hoto:@binance Asali:Twitter
Asali: Twitter

Mista Zhao wanda dukiyarsa ta kai Dala Biliyan 43 ya amsa laifin ka karya ka'idojin hana halasta kudin haram a kasar Amurka, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta sassauta hukuncin Chanpeng Zhao

Kotun da ke zamanta a birnin Seattle a Talatar nan ta yanke wa Chanpeng Zhao zaman gidan yarin watanni hudu maimakon shekaru uku da masu shigar da kara su ka nema, kamar yadda CNBC News ta ruwaito.

Kotun ta ce an sassauta hukuncin ne saboda dabi'a mai kyau ta Mista Zhao a baya.

Gabanin yanke hukuncin, Mista Zhao ya sanya hannu kan yarjejeniya da ma'aikatar Shari'a ta Amurka inda ya ajiye mukaminsa na shugaban Binance, tare da biyan Dala Biliyan 4.3.

Shugaban Binance din ya bayar da hakuri kan yadda kamfaninsa ya taimaka wajen badakalar kudaden haram da sauran kura-kurai.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N8bn: EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan Buhari a gaban kotu

Rahotanni sun ce duk da zai kasance a daure, arzikin Chanpeng Zhao zai ci gaba da karuwa sosai.

Binance ya dakatar da hada-hadar Naira

A baya kun ji cewa kamfanin hada-hadar kudade a yanar gizo na Binance ya dakatar da hada-hadar Naira a shirinsa na fita daga Najeriya.

Kamfanin ya shawarci yan Najeriya su gaggauta kwashe Nairar su, ko su sayi kudin wata kasar ko kuma su juyar da Nairar zuwa Dala domin gujewa asara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel