Ma su cewa Shugaba Buhari ya mutu sun susuce - Osinbajo
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa tsananin tsoron shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanya wasu Mutane sun kidime gami da susucewa.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, mafi akasarin jiga-jigai da ma su rike da madafan iko na kasar nan marasa martaba sun dukufa kan juya baya ga shugaba Buhari sanadiyar tsantsar akidarsa ta adawa da rashawa.
Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin halartar taron babbar cibiya ta kungiyoyin kasar nan magoya bayan shugaba Buhari da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Talatar da gabata.
Mataimakin shugaban kasar ya ke cewa, "tsananin shayin shugaba Buhari ya sanya ciwon hauka da zautuwa ya cimma wasu Mutanen kasar nan da a sanadiyar hakan suke faman ikirarin tuni shugaba Buhari ya riga mu gidan gaskiya kuma wanda yake jagorantar Najeriya a halin yanzu Angulu ce da kan Zabo".
Kamar yadda kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito, "wasu 'yan kasar nan dai musamman a yankin Kudancin Najeriya na yada jita-jitar cewa shugaban kasa Buhari ya jima da mutuwa, inda wani Mutum mai sunan Jibril dan kasar Sudan ke kwaikwayonsa."
KARANTA KUMA: Buhari ya gana da Shugaban kasar Switzerland kan dabarun ceto 'Yan Matan Chibok
A yayin gudanar da wannan babban taro da gwamnan jihar Legas ya halarta, Akinwumi Ambode ya bayyana cewa, yana da tabbaci kan wannan tafiya ta shugaba Buhari tare da Mataimakin sa Osinbajo za ta fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira ta fuskar inganci da habakar tattalin arzikin kasar nan.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari yayin zaman sauraron ra'ayin al'ummar Najeriya a wani bigire na daban yayin halartar taron sauyin yanayi a kasar Poland, ya yi raddi kan wannan lamari na Mutuwarsa da a cewar sa ba su da masaniyar ya kamata kuma bugu da kari ya sabawa kowane nau'i na addini.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng