Yanzu-yanzu: Wasu na rade-radin na mutu, ina nan daram-dam Buhari

Yanzu-yanzu: Wasu na rade-radin na mutu, ina nan daram-dam Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani mai zafi kan masu rade-radin cewa ya mutu a shekarun baya da yayi jinya a kasar Ingila. Ya bayyana cewa yana nan da rai kuma ba da dadewa ba, zan yi murnan ranan haihuwa na cika shekaru 76.

Legit Hausa ta samu wannan labari ne ta daga hadimin Buhari , Bashir Ahmad, inda yace:

"Daya daga cikin tambayoyin da aka min yau a ganawata da yan Najeriya mazauna Poland shine shin ni ne ko wani na ne kirkirarre. Wannan jahilcin ba abun mamaki bane - lokacin da nike jinya a bara, mutane da yawa sun so in mutu."

" Ni ne nan.... Ba da dadewa ba a cikin watan ne, zanyi murnan cika shekaru 76 kuma ina nan daram dam-dam."

Buhari yayi wannan furuci ne yayinda yake ganawa da yan Najeriya mazauna kasar Poland, a birnin Krakow.

Yanzu-yanzu: Wasu na rade-radin na mutu, ina nan daram-dam Buhari
Yanzu-yanzu: Wasu na rade-radin na mutu, ina nan daram-dam Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tawagar yakin neman zaben Atiku ta dira Sokoto

Wannan magana ta amsa tambayoyin wasu yan Najeriya cewa shin Muhammadu Buharin da muka sani ke mulki ko kuma wani Jibril daga kasar Sudan.

Labarin ya fara ne daga bakin shugaban masu son kafa kasar Biafra, da jagoransu Nnamdi Kanu. Kanu yace wani ne a Aso Rock ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kuma yayi barazanar fallasa yanda aka maida wani Jibril Adamu don maye gurbin mataccen shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar London.

Ya zargi cewa Jibril yayi kama da Buhari bambancin su kawai hanci mai fadi da hannayen yara da yake dasu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel