Sojoji Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa da Su a Arewacin Najeriya

Sojoji Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa da Su a Arewacin Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su a wasu garuruwa a yankin Arewacin Najeriya
  • Rundunar ta samu nasarar ne tare da wargaza maboyar masu garkuwa da mutanen da kuma kwato makamai masu yawa
  • A jiya Talata ne, 30 ga watan Afrilu, sanarwar ta fito daga rundunar sojan ta bakin kakakin ta, Laftanal Oni Olubodunde

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sojojin Najeriya sun yi nasarar wargaza sansanin 'yan ta'adda a jihar Taraba tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Sojoji
Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda a Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Dakarun sojojn kasar sun bayyana haka ne ta bakin jami'in ta na hulda da jama'a, Laftanal Oni Olubodunde, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar tsohon gwamnan Kano, Ganduje

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin sun kai hari wa ƴan ta'addan ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun samu bayanan ne kan wata maboyar ƴan ta'addan da ke garkuwa da mutane a Punkun cikin karamar hukumar Ussa.

Irin nasarar da sojojin suka samu

Rundunar sojan ta ce sun yi nasarar wargaza maboyar ta su tare da kwato bindigogi da sauran makamai.

Dadin dadawa rundunar ta yi nasarar cafke wani mai suna Dogo Manu da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a yankin, cewar jaridar Tribune

Sojoji sun ceto mutane a jihar Filato

A jihar Filato ma rundunar sojin ta yi nasar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Maraban Jama'a.

Majo Nantip Kakhom ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a jiya Talata, 30 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Nasrun MinalLah: Dakarun sojoji sun daƙile hari, sun sheƙe ƴan bindiga a ƙauyen Taraba

Ya ce sojojin an kira su ne ta waya a kan cewa an yi garkuwa da mutane kuma suka amsa kiran cikin gaggawa.

A lokacin da suka amsa kiran sun yi nasarar ceto Abdul Bello da Keyen Melody Yapshak daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun Operation Forest Sanity da ke jihar Zamfara sun samu nasarar ceto wasu mutum uku daga masu garkuwa da mutane bayan sun je sintiri maboyarsu

Sojojin sun garzaya har kauyen Danmarke dake karamar hukumar Gummi inda suka sakarwa 'yan bindigar wuta wanda hakan yasa suka arce da raunikan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel