Da duminsa: Boko Haram sun yi wa barikin soja 'zobe' a Borno
- Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai hari babbar barikin soji da ke Maiduguri a jihar Borno
- Sun kai harin wurin karfe 11:20 na daren ranar Litinin kamar yadda majiya daga rundunar soji ta sanar
- 'Yan ta'addan sun fara harbe-harbe amma sojojin sun fara martani kafin daga bisani sun gane cewa zobe aka yi musu
Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai hari wata babbar barikin sojoji da ke garin Maiduguri, a jihar Borno.
Majiya daga rundunar sojin ta sanar da jaridar The Cable cewa mayakan sun isa garin wurin karfe 11:20 na dare a ranar Litinin inda suka fara harbe-harbe zuwa cikin barikin.
Babu kakkautawa dakarun sojin suka fara mayar da martani amma sai dai tuni mayakan ta'addancin sun zagaye barikin, wata majiya ta tabbatar.
Tun farko dai mayakan Boko Haram sun fara kai hari wasu sassa na garin kafin daga bisani su isa barikin.
A yayin daa aka rubuta wannan rahoton, ana yaki tsakanin 'yan ta'addan da sojojin.
KU KARANTA: Bayan tube rawaninsa da marigayi Ado yayi, Sarkin Kano zai yi wa Babba-Dan-Agundi sarauta
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai wa tawagar sojoji da wasu masu ababen hawa hari, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A take suka kashe sojoji hudu, yayin da mutane da yawa suka bace a karamar hukumar Kaga ta jihar Borno, wata majiya daga jami'an tsaro ta sanar.
An gano cewa maharan sun tare masu ababen hawan a kusa da garin Mainok da ke Kafa wurin karfe 2 na yamma.
Sun halaka a kalla rayuka hudu tare da kone ababen hawan sojojin. Majiyar jami'an tsaron ta ce maharan sun yi awon gaba da makaman sojojin kuma masu tarin yawa har yanzu ba a san inda suke ba.
Kamar yadda majiyar ta kara da cewa, an kone wata motar daukar kaya tare da wata mota kirar Hilux a yayin harin.
"Sun bibiyi tawagar rundunar sojin amma jami'an RRS sun isa inda suka samu gawawwakin sojoji hudu. Abun akwai tashin hankali. Bayan ceton sauran da jami'an suka yi, sun kwato a kalla bindigogi kirar AK 47 guda 7," majiyar tace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng