Emefiele: Fayose Ya Caccaki DSS Kan Tayar Da Yamutsi a Kotu, Ya Nemi Tinubu Ya Dauki Mataki

Emefiele: Fayose Ya Caccaki DSS Kan Tayar Da Yamutsi a Kotu, Ya Nemi Tinubu Ya Dauki Mataki

  • Ana ci gaba da caccakar jami'an hukumar DSS biyo bayan rikicin da ya faru tsakaninsu da jami'an gidan yari a Kotu
  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yana cikin masu sukar abinda jami'an na DSS suka yi wajen shari'ar Emefiele
  • Fayose ya bayyana abinda jami'an na DSS suka yi a matsayin abin kunya da ka iya taɓa ƙimar gwamnatin Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikoyi, Jihar Legas - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi martani dangane da abinda ya faru tsakanin jami'an tsaro na farin kaya (DSS), da na hukumar gidajen gyaran hali (NCoS) a kotu bayan kammala shari'ar Emefiele.

A cikin wani bidiyo da ya yaɗu a Intanet, an ga jami'an na DSS na ja in ja da jami'an gidan gyaran hali kan wanda zai tafi da Emefiele.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

Fayose ya shawarci Tinubu kan matakin da ya kamata ya ɗauka kan DSS
Fayose ya nemi Tinubu ya ɗauki mataki kan DSS. Hoto: Ayodele Fayose, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jami'an DSS sun ƙi bin umarnin kotu

An bayyana cewa kotun ta bayar da belin Emefiele kan naira miliyan 20, tare da ba da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali kafin sharuɗan belin da kotun ta gindaya su cika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jami'an na DSS sun yi burus da umarnin kotun, inda suka dage cewa su ne za su tafi da shi ba jami'an gidan gyaran halin ba.

Hakan ta sa aka samu yamutsi wanda ya kai ga jami'an na DSS kyakketawa wani babban jami'in hukumar gidan gyaran halin kaya.

'Yan Najeriya da dama sun caccaki jami'an na DSS kan abinda suka yi gami da nuna rashin dacewar hakan.

Fayose ya nemi Tinubu ya ɗauki mataki a kan jami'an na DSS

Da yake mayar da martani kan lamarin, Fayose ya ce abinda jami'an DSS ɗin suka yi ya taka doka kuma zai iya ɓatawa gwamnatin Tinubu suna.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An Bayyana Mutanen Da Shugaba Tinubu Zai Naɗa a Matsayin Ministoci Kwanan Nan

Fayose ya yi martanin ne ta shafinsa na Twitter, inda ya nemi Tinubu ya ɗauki mataki cikin gaggawa don gudun kar su ɓata sunan gwamnatinsa kamar yadda suka yi wa gwamnatin baya.

Ya kuma nemi Shugaba Tinubu ya yi gaggawar sauya shugabancin hukumar, tare da neman a hukunta wanda ya kitsa abinda ya faru a babbar kotun Ikoyi da ke Legas ranar Talata.

Hukumar DSS ta fara bincike kan rikicin da ya faru a kotun Legas

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS), ta ce ta fara gudanar da bincike kan rikicin da ya faru a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi jihar Legas.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa hukumar DSS na mutunta ɓangaren shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel