Dele Farotimi: Shugaba Tinubu Ba Zai Nada Ministocin Da Za Su Gyara Najeriya Ba

Dele Farotimi: Shugaba Tinubu Ba Zai Nada Ministocin Da Za Su Gyara Najeriya Ba

  • Wani ɗan gwagwarmaya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dele Farotimi, ya ce Tinubu ba zai naɗa mutanen kirki a matsayin ministoci ba
  • Lauyan ya bayyana cewa dama can suna tunanin shugaba Tinubu zai yi wa Najeriya illa amma ya shiga Ofis ta tsiya
  • Ya ce mambobin jam'iyya mai mulki ba su kishin ƙasar nan kuma su ne mutanen da za a naɗa a matsayin ministoci

Dele Farotimi, mai fafutuka kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, ya ce shugaba Bola Tinubu ba shi da niyyar nada ministocin da za su gyara Najeriya.

A wata hira da ya yi da 90Minutes Africa a ranar Lahadi, Farotimi ya ce ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba su da kishin kasar nan a zuciyoyinsu.

Dele Farotimi da Bola Ahmed Tinubu.
Dele Farotimi: Shugaba Tinubu Ba Zai Nada Ministocin da Zasu Gyara Najeriya Ba Hoto: Dele Farotimi, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A ‘yan kwanakin da suka gabata an yi ta tattaunawa da kace nace kan jinkirin shugaban ƙasa wajen mika jerin sunayen ministoci ga majalisar dattawa domin tantancewa.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya Dole Shugaba Tinubu Ya Bayyana Sunayen Ministocinsa Nan Da Ranar Juma'a

A halin yanzu, shugaban na da ragowar daga nan zuwa ranar Juma'a, 28 ga Yuli, don gabatar da ministocinsa, bisa ga wa'adin kwanaki 60 na tsarin mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane irin mutane Tinubu zai naɗa a matsayin Ministoci?

Da yake maida martani kan wannan ci gaban, lauyan kuma ɗan gwagwarmaya ya yi tir da cewa jerin da ake jira daga Tinubu ba zai canza arziki ko sa'ar ƙasar nan ba.

The Cable ta rahoto Dele Farotimi na cewa:

"Gidajen su (masu mulku) na kasahen waje, da zaran sun kamu da mura sai su hau jirgi su tashi zuwa kasashen waje don ganin likitocinsu, kuma ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a Najeriya."
"Wasunmu sun san tun farko Tinubu zai yi wa kasar nan illa. Mun gargadi kowa kuma mutane sun saurari gargaɗinmu. Sun yi duk mai yuwuwa wajen ganin bai ci zaɓe ba amma ya bi wata hanyar ta dole ya shiga Ofis."

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 Kacal a Najeriya, Fitaccen Malami Ya Faɗi Gaskiya

"Me kuke tunani daga APC da sauran masu shirin ruguza ƙasarmu, zasu tabbata sun haɗa kai wuri ɗaya wajen ganin shugaban ƙasa ya naɗa mutanen da zasu ɗaga waɗanda suka taimake shi."

Micheal Bamidele, shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, a ranar Talata ya ce shugaban kasar zai aika jerin sunayen ministocinsa zuwa zauren majalisar dokoki cikin sa'o'i 48 masu zuwa.

NLC: Kungiyar Kwadugo Ta Sanar da Tsunduma Yajin Aiki Daga Watan Agusta

A wani rahoton kuma Ƙungiyar kwadugo NLC ta sanar da ranar shiga yajin aikin gama gari idan FG ta gaza biyan buƙatunta.

NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 ta sake nazari kan tsare-tsarenta da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel