Hukumar DSS Ta Fara Bincike Kan Rigimar da Ta Faru a Kotun Legas

Hukumar DSS Ta Fara Bincike Kan Rigimar da Ta Faru a Kotun Legas

  • Hukumar DSS ta bayyana cewa tuni ta fara bincike kan rikicin da ya faru a babbar Kotun tarayya mai zama a Ikoyi, jihar Legas
  • A wata sanarwa, kakakin DSS na ƙasa ya ce hukumar tana mutunta bangaren shari'a domin yana da muhimmanci
  • Idan baku manta ba jami'an DSS da jami'an kula da gidajen gyaran hali sun samu saɓani ranar da aka gurfanar da Emefiele

FCT Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce za ta gudanar da bincike kan rikicin da ya barke tsakanin jami’anta da na hukumar gidan yari (NCoS) a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a ranar 25 ga watan Yuli.

A ranar Talata ne Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya gurfana a gaban babbar kotun kuma Alkali ya bayar da belinnsa kan N20m.

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

Rigimar jami'an DSS da na gidan gyaran hali.
Hukumar DSS Ta Fara Bincine Kan Rigimar da Ta Faru a Kotun Legas Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mai shari'a Nicholas Oweibo, ya yanke hukuncin cewa a ci gaba da tsare Emefiele a gidan gyaran hali, har sai an cika sharuddan belinsa amma jami’an DSS suka dage sai sun tafi da shi.

Sakamakon haka, hatsaniya ta barke tsakanin jami’an NCoS da hukumar DSS a harabar kotun, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar DSS ta girmama bangaren shari'a

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya ce hukumar DSS na mutunta bangaren shari’a kuma ba za ta yi ganganci da kuskuren yi wa shari'a zagon ƙasa ba.

Daily Trust ta rahoto kakakin DSS, Afunanya na cewa:

"DSS ta ɗauki bangaren shari’a a matsayin wani muhimmin bangare na gina kasa, ci gaban kasa da kuma kula da harkokin tsaro,”

Kara karanta wannan

Shari'ar Emefiele: Fayose Ya Ba Tinubu Shawara Kan Matakin Da Ya Kamata Ya Ɗauka a Kan DSS

“Har ila yau, hukumar tana da kyakkyawar alakar aiki tare da sauran hukumomin tsaro da ke kokarin tabbatar da bin doka da oda ciki har da hukumar NCoS."

Zamu gudanar da binciek kan lamarin - DSS

Afunanya ya ƙara da cewa jami’an hukumomin biyu sun nuna “zafin rai wanda bai dace ba” inda ya ce hukumar DSS ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

"Zamu yi bincike ne da nufin gano rawar da kowane jami'i ya taka tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan ta kama, da kuma ɗaukar darussa domin kiyaye gaba," in ji shi.

Allahu Akbar, An Gano Jaririn da Aka Sace a Babbar Kasuwar Arewacin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa an gano jaririn da aka ɗauke a kasuwar Kure da ke Minna a jihar Neja.

Mahaifin jaririn ya ce an gano shi a cikin bola kusa da caji ofis ɗin 'yan sanda na Gauraka da ke ƙaramar hukumar Tafa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Hukumar DSS Ta Sake Cafke Godwin Emefiele

Asali: Legit.ng

Online view pixel