Tirkashi: Miji Ya Samu Karuwar 'Ya'Ya 4 Bayan Ya Yi Niyyar Zubar Da Cikin A Baya

Tirkashi: Miji Ya Samu Karuwar 'Ya'Ya 4 Bayan Ya Yi Niyyar Zubar Da Cikin A Baya

  • Wani matashi da ya yi niyyar zubar da cikin matarsa ya samu karuwar 'ya'ya hudu a jihar Oyo
  • Matashin mai suna, Dauda Olamilekan ya bayyana cewa ba shi da halin da zai dauki nauyin yaran
  • Matar mai suna Rukaiyat ta na cikin koshin lafiya da 'ya'yanta maza biyu da mata biyu a asibiti

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Wani magidanci mai suna Dauda Olamilekan da ya yi niyyar zubar da cikin matarsa a lokacin da take da juna biyu yanzu ta haifi jarirai 'yan hudu.

Matashin lokacin da ya yi niyyar zubar da cikin ya koka kan irin halin da ake ciki a kasar shiyasa ba ya son haihuwar.

Miji Ya Shiga Yanayi Bayan Ya Samu Karuwar 'Ya'Ya 4 A Oyo
Matashin Ya Koka Da Dawainiyar Yaran Inda Ya Nemi Taimakon Jama'a Da Gwamnati. Hoto: Information Nigeria.
Asali: Facebook

Matar, Rukayat mai shekaru 27 ta haifi 'ya'yan ne a ranar Alhamis 20 ga watan Yuli a Ogbomosho da ke jihar Oyo, New Telegraph ta tattaro.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Rasuwar Ma'aurata, 'Yayansu Da Mutane 2 a Anambra

Mijin ya koka kan yanayin rayuwa bayan samun karuwar

Dauda da mai dakinsa suna zaune ne a unguwar Ijeru da 'ya'yansu guda biyu kadai a duniya, Aminiya ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Magidancin ya tabbatar da cewa a yanzu da ta haifa masa wadannan 'ya'ya ba shi da halin da zai dauki dawainiyarsu inda ya bukaci jama'a su taimaka masa.

Olamilekan ya ce ya na bukatar taimako daga gwamnati da sauran jama'a saboda sana'ar fawa yake yi kuma ba wani samu ya ke ba, ya ce ma'aikatan asibitin ne suka hana shi zubar da cikin.

Ya bayyana yadda ya yi niyyar zubar da cikin

A cewarsa:

"Mun taba zuwa daukar hoton cikin, a nan ne ma'aikatan lafiya suka tabbatar mini cewa 'ya'ya hudu take dauke da su.
"Daga ranar na yanke hukuncin zubar da cikin saboda ba ni da halin ci gaba da daukar dawarniyarsu, amma ma'aikatan asibitin suka hana ni daukar wannan mataki.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Matashi A Kokarin Sace Yaro A Katsina, Ba Su Yi Nasarar Sace Yaron ba

"Kuma sun taimaka mana sosai har zuwa lokacin da Rukayat ta haihu a asibitin."

Rukayat da jariranta maza biyu da mata biyu suna cikin koshin lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola da ke Ogbomosho cikin jihar Oyo, cewar Daily Post.

Farfesa Ya Bukaci Tinubu Ya Gudanar Da Kidayar Dabbobi Don Sanin Adadinsu, Ya Bayyana Alfanu

A wani labarin, wani Farfesa ya bukaci Shugaba Tinubu da ya kaddamar da kidayar dabbobi don sanin adadinsu a kasa.

Farfesa Olajide Babayemi na jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo ya bayyana haka ga 'yan jaridu a ranar Laraba 21 ga watan Yuni a Lagos.

Ya ce sanin adadin dabbobin zai taimakawa gwamnati wurin sanin yadda za ta tsara abubuwa kamar na mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel