Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma’aikacin Dangote da ya zama gwamna, AA Sule
An haifi Injiniya Abdullahi Alhaji Sule a ranar 26 ga watan Disamba a garin Gudi Station, yaammancin Akwanga da ke jihar Nasarawa. Mahaifinsa ne Hakimin garin yayinda kakansa ya kasance Sarkin garn Gudi.
Injiniya A. A Sule ya kasance zababben gwamnan jihar Nasarawa a zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.
Sule yayi takara ne a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Asali: UGC
Ya samu yawan kuri’u 327,229 wajen doke sauran yan takara 28 da suka fito neman kujerar gwamna.
Zababben gwamnan yayi mafi akasarin rayuwarsa ne a kasar waje bayan yayi ta samun nasarori a fannin karatunsa kasancewarsa mai kwazo da kokari kafin daga baya dawo kasar Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP
Kafin fitowarsa takarar kujerar gwamna, Sule ya kasance ma’aikaci a kamfanin Dangote, wanda ya kasance mafi girma a kasar. A wannan kamfani na Dangote, Sule ya kasance Manajan Darakta.
Kafin zuwansa kamfanin Dangote, Sule yayi aiki a manyan kamfanoni da dama a kasar, kama daga na kera karafuna, kamfanonin man fetur da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng