'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Biyu a Birnin Tarayya Abuja

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Biyu a Birnin Tarayya Abuja

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun bi cikin tsakar dare sun sace wasu mutum biyu a yankin Mpape na birnin tarayya Abuja
  • Ƴan bindigan dai sun dira cikin yankin ɗauke da miyagun bindigogi suna ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi kafin su sace mutanen
  • Sai dai, jami'an ƴan sanda sun bi bayan ƴan bindigan inda suka ceto mutum biyun da aka sace yayin da za su miƙa su hannun iyalansu

FCT, Abuja - Ƴan bindiga sun sace aƙalla mutum biyu a yankin Mpape cikin birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan bindigan sun dira a yankin ne cikin tsakar dare inda suka sace mutum biyu.

Yan bindiga sun sace mutum biyu a Abuja
Josephine Adeh, kakakin rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja Hoto: Thecable.com
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin mai suna Yakubu ya bayyana cewa ƴan bindigan su shida ne suka diro yankin ɗauke da bindigogi.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Yi Gumurzu Da 'Yan Bindiga Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace a Arewacin Najeriya

"Da misalin ƙarge 1:00 na daren yau, ƴan bindiga mutum shida sun shigo yankin mu suna ta harbin bindiga inda suka ɗauke mutum biyu." A cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta ƙara da cewa ƴan sanda sun ceto mutum biyun da aka sace inda tace nan bada daɗewa ba za a sada su da iyalansu.

Adah ta bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an cafke ƴan bindigan da ake zargi.

"Jami'an ƴan sanda na Mpape da na tawaga ta musamman daga hedikwata sun mayar da martani nan da nan." A cewarta.
"Sun matsawa ƴan ta'addan wanda hakan ya tilastu su suka bar mutanen da suka sace. Nan bada jimawa ba za a sada su da iyalansu. Muna ci gaba da bin sahun waɗanda ake zargin."

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Wata Likita Bayan Yin Basaja A Matsayin Marasa Lafiya

Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga a Jihar Plateau

A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya masu wanzar da zaman lafiga a jihar Plateau, sun samu nasarar murƙushe wasu miyagun ƴan bindiga a jihar.

Dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun halaka ƴan bindigan mutum uki tare da ƙwato makamai a hannunsu a wani kwanton ɓauna da suma yi musu a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng