Gwamna Soludo Ya Ba da Umarnin Masana Halayyar Dan Adam Su Zauna da Dalibar da Ta Jirkita Sakamakon JAMB

Gwamna Soludo Ya Ba da Umarnin Masana Halayyar Dan Adam Su Zauna da Dalibar da Ta Jirkita Sakamakon JAMB

  • Gwamnan jihar Anambra ya umarci a zauna da dalibar da ta yi karin makin UTME don jin inda take da matsala ta kwakwalwa ko hali
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka tabbatar da ta yi karin sakamakon jarrabawar da kuma jawo cece-kuce a kasar nan
  • ‘Yan Najeriya sun shiga mamaki bayan da dalibar ta bayyana cewa tabbas ta jirkita sakamakon nata ta wata hanyar fasaha

Jihar Anambra - Gwamnan Anambra Chukwuma Soludo ya bayar da umarnin mika Mmesomma Joy Ejikeme, dalibar da ta jirkita sakamakon jarabawarta na UTME ga farfesa a fannin ilimin halin dan Adam.

Soludo, ya bayyana hakan ne a cikun wata wasikar da ya tura wa Shugabar Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Anglican Nnewi inda Mmesoma ta yi karatu.

Wasikar ta bayyana bukatar fara shirin ba daura dalibar kan turba nan take, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

“Zan Dauki Nauyin Mmesoma Ejikeme”: Miloniya Zai Tura Yarinyar Da Ta Kirkiri Sakamakon JAMB Dinta Waje Karatu

An umarci zama da dalibar da ta yi karin makin JAMB
Dalibar da ta kara makin JAMB na bogi | Hoto: The Nation Newspaper
Asali: UGC

Idan baku manta ba, dalibar a ranar Alhamis, 6 ga Yuli, 2023 ta yarda cewa ta yi amfani da sakamakon manhaja wajen jirkita sakamakon jarrabawarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Batun gwamna kan dalibar

A cikin wasikar mai dauke da sa hannun kwamishiniyar ilimi, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, gwamnan ya ce umarnin ya biyo bayan daya daga cikin shawarwarin da kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin dalibar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Umarnin ya yi daidai da daya daga cikin shawarwarin da kwamitin da gwamnatin jihar Anambra ta kafa domin gudanar da bincike kan lamarin, biyo bayan fitar sakamakon bogin da ya haifar da cece-kuce da tada hankalin al’umma.”

‘Yan Najeriya sun damu da batun dalibar Anambra

Idan baku manta ba, a makon da ya gabata ne ‘yan Najeriya ke ci gaba da cece-kuce da nuna damuwa bayan da soke sakamakon jarrabawar Ejikeme.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: An kai karar Abba Gida-Gida Amurka, China da EU kan gallazawa Kanawa

Dalibar ta ce, ita ce ta fi kowa cin jarrabawar UTME a bana, lamarin da JAMB ta musanta tare da bayyana hujjoji.

Ya zuwa yanzu, an kange dalibar daga rubuta jarrabawar har na tsawon shekaru uku a matsayin ladabtarwa.

Mahaifin dalibai Mmesoma da ta yi karyar cin JAMB ta fito ya ba hakuri

A wani labarin, mahaifin Mmesoma Ejikeme, dalibar da ta jirkita sakamakon jarrabawarta na JAMB, ya fito fili ya nemi gafarar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) da ma ‘yan Najeriya baki daya.

Kamar yadda aka gani a wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), ya ce da far dai ‘yarsa ta shirga masa karya don haka yanzu da ya san gaskiya, yana fatan JAMB ta yafewa ‘yarsa.

A baya, yarinyar ta yi ikirarin cewa, ta lashe sakamako mafi yawa na UTME na 2023, lamarin da ya jawo cece-kuce bayan da hukumar JAMB ta ce ba haka bane.

Kara karanta wannan

Ahaf: Mahaifin dalibar da ta jirkita sakamkon JAMB ya fadi gaskiya, ya nemi afuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel