“Zan Dauki Nauyinta Zuwa Kanata”: Miloniya Ya Tabbatar Da Taimakawa Mmesoma

“Zan Dauki Nauyinta Zuwa Kanata”: Miloniya Ya Tabbatar Da Taimakawa Mmesoma

  • Wani miloniyan Najeriya ya bayyana cewa zai dauki nauyin karatun Mmesoma Ejikeme yayin da ake takaddamar kirkirar sakamakon jarrabawarta
  • Mutumin wanda ya bayyana cewa zai kira yarinyar sannan ya bata shawara sosai ya ce ta kwaikwayi gurbatattun shugabannin Najeriya ne
  • Yan Najeriya da dama sun jinjina mashi kan taimakon da ya yi wa matashiyar wacce ta rasa gudunmawa da dama tun bayan da ya tabbata ta kirkiri sakamakon JAMB dinta ne

Wani attajirin miloniya a Najeriya kuma mai zuba hannun jari a harkar 'crypto', wanda aka fi sani da BitcoinChief, ya bayyana cewa duk da sabbin abubuwan da aka gano kan sakamakon jarrabawar JAMB din Mmesoma Ejike, yana nan a kan bakarsa na daukar nauyin karatunta.

A wani rubutu da ya yi a Twitter, mutumin ya bayyana cewa hatta Najeriya tana murna da zabar shugabanni masu aikata rashawa da takardun shaidar kammala karatu na bogi. BitcoinChief ya bayyana cewa zai kira Mmesoma sannan ya yi magana da ita.

Kara karanta wannan

Ahaf: Mahaifin dalibar da ta jirkita sakamkon JAMB ya fadi gaskiya, ya nemi afuwa

Attajiri dan Najeriya na shirin tallafawa Mmesoma
“Zan Dauki Nauyinta Zuwa Kanata”: Miloniya Ya Tabbatar Da Taimakawa Mmesoma Hoto: @gaiuschibueze
Asali: Twitter

Attajiri na kan bakarsa na daukar nauyin karatun Ejikeme

Ya kara da cewar zai fahimtar da ita don ta gane cewa yawan makin da mutum ya samu a JAMB ba shine ke nufin makomarsu ko abun da za su zama ba. A wani rubutu da ya fara saki, ya ce zai dauki nauyin yarinyar zuwa US, UK ko Kanada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Attajirin ya ce akwai misalai marasa kyau da dama a kasar wanda matashiyar ta yi koyi da su, kuma cewa ya kamata a fara hukunta wadannan mutane tukuna. Kalamansa:

"Ta yi kuskure kuma ya zama dole ayi mata gyara sannan a nuna mata hanya madaidaiciya saboda gaba!"

Kalli wallafarsa a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

@samuel_stephenc ya ce:

"Wannan shine yasa nake son ka ba tare da sharadi ba, ka zame mani madubin duba da wannan karamci naka. Nagode."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kamfanin Innoson Ya Janye Tallafin Karatun Da Ya Baiwa Mmesoma

@bechiny:

"Na yarda da hukunta mai laifi tare da kin yi mai afuwa ko karrama shi. Ta haka ne kawai kasashe masu hankali suke cimma da tabbatar da doka da oda. Alkalai a kasashe masu tunani za su tura danginsu gidan yari ne saboda doka na kan kowa daidai. Tana bukatar wannan."

@eduhandsome_ ya ce:

"Allah ya yi maka albarka dan uwa. Mu yan masarautar Anambra muna godiya a gareka saboda wannan soyayya da taimako da ka yi wa mmesoma Ejikeme. Chukwu Gozie gi nnam."

Kamfanin Innoson ya janye tallafin karatun da ya baiwa Mmesoma

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kmotoci na Innoson ya janye tallafin karatu da ya baiwa Joy Mmesoma Ejikeme bayan kwamitin bincike na gwamnatin Anambra ya bayyana cewa sakamakon jarrabawarta na UTME na bogi ne.

Kwamitin ya saki sakamakon bincikensa a ranar Juma'a, yana mai bayyana cewa Mmesoma ta yarda cewa ta kirkiri makin ta ne. =

Asali: Legit.ng

Online view pixel