Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Fito

Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Fito

  • Wani sanannen ɗan Najeriya, Harrison Gwamnishu, ya je gidansu Mmesoma Ejikeme bayan ta sharɓi kuka kan sakamakon da ta sauya
  • Da yake tabbatar mata da cewa ɗan Adam na yin kuskure, Harrison ya bayyana cewa ta yi alƙawarin bayar da haƙuri kan aika-aikar da ta yi
  • Ƴan Najeriya da dama da suka yi arba da sabon bidiyon na ta sun yi ta mamakin dalilin da ya sanya ta ƙara wa kanta maki bayan ta samu maki mai yawa

Wani sananne kuma mai bayar da agaji, Harrison Gwamnishu, ya yi wani ɗan ƙaramin bidiyo inda ya roƙi ƴan Najeriya da su dai na caccakar Mmesoma Ejikeme.

Mutumin ya bayyana cewa ya samu kiran gaggawa ne daga yarinyar, inda ta yi niyyar yi wa kanta illa saboda ƙarin makin da ta yi domin ba za ta iya fuskantar abun kunyan da ta yi ba.

Kara karanta wannan

"Mun Same Shi Lullube Da Zuma": Mahaifin Jaririn Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Mahaifiyarsa Ya Bayyana Yadda Ya Rayu Sa'o'i 24 Bayan Ta Rasu

Mmesoma Ejikeme ta yi alkawarin bada hakuri
Mmesoma Ejikeme ta natsu a cikin sabon bidiyon da aka saki Hoto: @harrison_gwamnishu
Asali: Instagram

Mmesoma ta yi kuka sosai a lokacin wayar da suka yi

Bayan ya amsa kiran wayar da ta yi masa, Harrison ya garzaya zuwa gidansu domin tabbatar mata da buƙatar ta kare lafiyar ƙwaƙwalwarta, domin dama an san ɗan Adam da yin kuskure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin bidiyon ya bayyana cewa yarinyar ta shirya bayar da haƙuri ga ƴan Najeriya kan yadda ta ƙara wa kanta maki.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin da aka bayyana.

soyoufoundeve ya rubuta:

"Idan har da gaske ta aikata hakan, ina son sanin dalilinta na yin hakan saboda 249 da ta samu ya ishe ta samun jami'ar da ta ke so. Maki 200 da ƙanwata ta samu ta yi murna akai."

miknorwings ya rubuta:

"Ina ji a jikina cewa yarinyar nan tursasa ta aka yi ta faɗi abinda ake so."

Kara karanta wannan

Wane Hali Yarinya Yar Shekara 14 da Tsohon Gwamna Ya Aura a Najeriya? Bayanai Sun Fito

cartoonmakun ya rubuta:

"Dukkanmu muna yin kuskure a rayuwa. Abinda ta ke buƙata shi ne ta mayar da hankali ta zama mutumiyar kirki. Yakamata a nuna mata so tun da muna nunawa waɗanda ma su ke yin kura-kuran da suka fi nata."

visazmigration_llc said:

"Ko tantama babu tana da wayau, amma ku ja mata kunne, ku bata shawarwari da ɗora ta kan daidai, idan ba haka ba wasu za su sake maimaita abinda ta yi."

Miloniya Zai Dauki Nauyin Karatun Mmesoma Ejikeme

A wani labarin na daban kuma, wani miloniya ya sha alwashin ɗaukar nauyin karatun Mmesoma Ejikeme zuwa ƙasar waje.

Attajirin mai harkar 'Crypto' wanda aka fi sani da suna BitcoinChief ya bayyana cewa yana nan a kan bakansa na kai ta karatu zuwa ƙasar Canada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel