Na Yi Nadamar Goyon Bayan Jam'iyyar APC, Jaruma Oshodi-Oke

Na Yi Nadamar Goyon Bayan Jam'iyyar APC, Jaruma Oshodi-Oke

  • Jarumar fim ɗin Nollywood Ibironke Oko Anthony da aka fi sani da Ronke Oshodi-Oke ta ce APC ta watsa mata ƙasa a fuska
  • Ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da shahararren jami'in yaɗa labaran nan Chude Jideonwo
  • Ta ce jam'iyyar APC ta gaza a mulkin da ta gudanar cikin shekaru takwas na baya da suka gabata

Fitacciyar jarumar fim ɗin Nollywood, Ibironke Ojo-Anthony, wacce aka fi sani da Ronke Oshodi-Oke, ta bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki, ta gaza a cikin shekaru takwas ɗin da ta yi mulki a baya.

Ta ce ta yi nadamar goyon baya da kuma tallata jam'iyyar da ta yi bayan abinda ya faru a zanga-zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jarumar fim ta ce ta yi da na sanin tallata APC a baya
Jaruma Oshodi-Oke ta ce ta yi nadamar tallata jam'iyyar APC da ta yi a baya. Hoto: Ronke Oshodi-Oke
Asali: Facebook

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da fitaccen jami’in yaɗa labaran nan Chude Jideonwo.

Kara karanta wannan

Wane Hali Yarinya Yar Shekara 14 da Tsohon Gwamna Ya Aura a Najeriya? Bayanai Sun Fito

Dalilin gudanar da zanga-zangar EndSARS

A watan Oktoban 2020, matasan Najeriya musamman mazauna Legas, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rusasshiyar hukumar jami'an 'yan sanda na musamman wato SARS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar sun buƙaci a kawo karshen cin zarafin da 'yan sandan na SARS ke yi musu. Sun kuma yi amfani da damar wajen neman ingantaccen shugabanci daga masu mulki.

Oshodo-Oke ta kuma ƙara da cewa, ta ji takaicin maganar da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi a lokacin zanga-zangar.

Ta ce ba ta ji ɗaɗin kalaman da gwamnan Legas ya yi ba

'Yar wasan kwaikwayon ta ce ba ta ji ɗaɗin kalaman da ya yi na cewa babu wanda aka kashe yayin zanga-zangar ba.

A cewarta:

“Ina son APC. Ni masoyiyar APC ce, jiki da ruhi na. Na yi tunanin cewa APC za ta kai Najeriya zuwa mataki na gaba."

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

“Dalilin haka ne ma ko a lokacin da muke yin yaƙin neman zaɓe, ban karɓi kuɗi da yawa ba. Ba kuɗi na zo nema ba, ina hangen abinda zai faru a gaba ne."

Ta ƙara da cewa ta yi wa APC uzuri sosai, saboda a tunaninta shekaru takwas, sun yi kaɗan a gyara Najeriya.

Sai dai ta ce a lokacin zanga-zangar EndSARS, ta rasa duk wani ƙwarin gwiwar da take da shi a kan APC kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Dattijuwa ta tsinewa Peter Obi da jam'iyyarsa Labour

Legit.ng a baya ta kawo muku wani labari kan wata dattijuwa da ta tsinewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Peter Obi, da jam'iyyarsa ta Labour.

Tsohuwar mai shekaru 74 ta koka kan yadda jam'iyyar ta manta da ita duk da harbin bindigar da ta sha a lokacin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel