Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin majalisa Ghali Na’abba bai mutu ba, yana nan da ransa

Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin majalisa Ghali Na’abba bai mutu ba, yana nan da ransa

- Sabanin yadda aka ta bazawa a shafukan zumunta, tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba na nan da ransa

- Binciken Jaridar Leadership ta gano labarin na bogi ne mara tushe balle makama

- Tun a daren jiya Alhamis ne dai aka fara rade-radin mutuwar dan siyasan

Ba kamar yadda kafafen sada zumuntar zamani suka dinga wallafawa ba tun a daren jiya Alhamis, tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba bai mutu ba.

Binciken Jaridar Leadership ta gano labarin na bogi ne mara tushe balle makama.

Jita-jitar mutuwar tsohon dan majalisar ya bazu ne a yanar gizo bayan wasu kafafen yada labarai sun sanar da mutuwarsa.

Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin majalisa Ghali Na’abba bai mutu ba, yana nan da ransa
Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin majalisa Ghali Na’abba bai mutu ba, yana nan da ransa
Asali: Facebook

Na'abba ya yi aiki a majalisar ne yayin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin kakakin majalisar wakilai ta tarayya.

KU KARANTA KUMA: Ba zan daina kukan rashin Ubale ba – Yakubu Muhammed ya yi zantuka masu taba zuciya kan marigayin

A gefe guda, mun ji cewa Gidauniyar Kwankwasiyya, ta tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta bayyana damuwarta bisa yadda gwamnatin Kano ta yi fatali da kyautar da ta ba ta.

Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne Kwankwaso ya sanar da bai wa gwamnatin jahar Kano kyautar wani asibiti da ya gina mai suna Amana domin a dinga killace masu cutar Coronavirus.

Asibitin yana nan ne a kan titin Miller, kuma yana cin gado 30 ne, kamar yadda kaakakin dan takarar gwamnan Kano a PDP, Abba Yusuf, Ibrahim Adam ya sanar a ranar 20 ga watan Afrilu.

Sanawar ta kara da cewa asibitin na cike ne da kayan aiki, wadanda Kwankwaso ya sanya a ciki tun zamanin da yake majalisar dattawa.

Amma har yanzu gwamnatin jahar Kano bata amshi wannan kyauta da Kwankwaso ya yi mata ba, kuma bata yi amfani da shi ba, kamar yadda kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana.

Don haka suka zargi Ganduje da yin siyasa da rayukan jama’an Kano ta hanyar kin karbar gudunmuwar da suka bayar domin ceton rayukan Kanawa da lafiyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel