Borno: EFCC Ta Kama Dattijo Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har Miliyan 12, Ya Musanta Aikata Laifin

Borno: EFCC Ta Kama Dattijo Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har Miliyan 12, Ya Musanta Aikata Laifin

  • Hukumar EFCC reshen jihar Borno ta gurfanar da wani mutum da ake zargin cinye gadon marayu a Maiduguri
  • Hukumar ta ce ana zargin Isiyaku Ibrahim da handame makudan kudade na marayu da suka kai har N12m
  • Alkalin kotun, Usman Fadawu ya tsare wanda ake zargin tare da dage sauraran karar zuwa 12 ga watan Yuli

Jihar Borno - Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) reshen jihar Borno ta kama wani dattijo da ake zargi da badakalar makudan kudade har N12m.

Wanda ake zargin mai suna Isiyaku Ibrahim an tuhumeshi da badakalar kudade tare da gurfanar da shi a gaban alkalin babbar kotun jihar Borno, Usman Fadawu.

EFCC ta kama dattijo da ake zargi da handame dukiyar magada a Borno
Dattijon Da EFCC Ta Kama Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har Miliyan 12. Hoto: EFCC.
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da mutumin kan zargin handame gadon marayu

A cikin takardar tuhuma da hukumar ta gabatar tana cewa:

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Shiga Tasku a Yayin Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Sake Fara Bincike Kan Bidiyonsa Na Daloli

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kai Isiyaku Ibrahim, watarana tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019 a Jajere kan hanyar Baga cikin Maiduguri da ke jihar Borno an baka amanar kadara na marigayi Muhammad Isiyaku.
"Kadarorin sun hada da gidaje uku da filaye biyu da ke dauke da shaguna bakwai da gidajen biredi biyu.
"Sauran sun hada da katon fili guda daya da manyan tankuna biyu da katon injin ba da wutar lantarki wanda jimillar su ta kai N12m.
"Wanda ka handame su ba tare da duba yanayin iyalan mamacin ba, hakan babban laifi ne kuma ya sabawa sashe 308 da 309 na dokokin jihar Borno."

Wanda ake zargin bai amince da tuhume-tuhumen da ake zarginshi ba

Wanda ake zargin ya musanta tuhume-tuhumen da ake zarginshi da su, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

Lauyan masu karar, S. O Saka ya roki kotun ta ci gaba da tsare shi a gidan kaso tare da saka ranar ci gaba da shari'ar.

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata: An Kama Kwamishinan Ganduje Kan Badakalar Biliyan 1

Alkalin kotun, Usman Fadawu ya tsare wanda ake zargin a gidan kaso tare da dage sauraran karar zuwa 12 ga watan Yuli.

Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Da Ya Kange Matarsa Na Tsawon Shekaru Babu Abinci

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda ta kama magidanci kan zargin kange matarsa na tsawon shekaru ba tare da kulawa ba.

Wanda ake zargin mai suna Abdullahi Isa ya daure matarsa na tsawon shekaru biyu ba tare da ba ta abinci ba.

Mai rajin kare hakkin dan Adam, Kwamred Lucy Yunana ta kwashi matar zuwa asibiti don duba lafiyarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel