Jami'an Tsaro Sun Yi Musayar Wuta da Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina

Jami'an Tsaro Sun Yi Musayar Wuta da Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara a Katsina

  • Jami'an tsaron haɗin guiwa sun samu nasarar ceto fasinjoji 17 bayan musayar wuta da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Batsari a Katsina
  • Wata majiya daga rundunar sojoji ta ce jami'an sun kai ɗauki ne bayan samun kiran gaggawa daga yankin ranar 11 ga watan Mayu, 2024
  • Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa jami'an sojoji na ci gaba da aiki ba da dare ba rana domin tabbatar da tsaro ya dawo a faɗin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da fasinjoji 17 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yankin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Wata majiya mai tushe daga rundunar sojoji ta bayyana cewa jami'an tsaron sun samu wannan nasara ne bayan samun kiran gaggawa ranar 11 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

Sojojin Najeriya.
Jami'an Tsaro sun ceto fasinjoji 17 daga hannun ƴan bindiga a Katsina Hoto: Nigeria Army HQ
Asali: Twitter

Ya ce dakarun rundunar soji ta 9 ne suka kai ɗauki bayan samun bayanai tare da haɗin guiwar ƴan sanda, ƴan sa'kai na jiha, mafarauta na musamman da mafarautan Batsari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, bayan samun rahoton harin ƴan bindiga, haɗakar jami'an tsaron suka haɗu suka kai ɗaukin gaggawa a yankin Batsari.

Jami'an tsaro sun fafata da ƴan bindiga

Da isar dakarun, suka fara musayar wuta da ƴan bindigar wanda ya tilasta wa maharan arcewa zuwa dazuka mafi kusa tare da barin waɗanda suka sace a wurin.

Majiyar ta ce bayan ceto fasinjojin, jami'an tsaron sun mika waɗanda aka kuɓutar ga jami'an gwamnatin ƙaramar hukumar Batsari, rahoton Ƙatsina Mirror.

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta ce tuni aka ƙara tura jami'an sojoji a yankunan domin kakkaɓe ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Rikicin shugabancin daba: Mutum 3 sun mutu yayin da wani faɗa ya ɓarke a Kano

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ranar Lahadi, ya ce dakarun sojoji na ci gaba da aiki don magance ayyukan ƴan ta'adda.

Yan bindiga sun kashe malami a Zamfara

A wani rahoton na daban, an ji 'yan bindiga sun kai hari kan manoma a kananan hukumomin Maradun da Tsafe a jihar Zamfara ranar Alhamis da ta wuce.

Rahoto daga yankin ya nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban malamin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel