Ruwan Sama Mai Ƙarfi Haɗe Da Iska Ya Lalata Sama Da Gidaje 100 a Jihar Kebbi

Ruwan Sama Mai Ƙarfi Haɗe Da Iska Ya Lalata Sama Da Gidaje 100 a Jihar Kebbi

  • Mamakon ruwan sama mai haɗe da iska, ya lalata sama da gidaje 100 a jihar Kebbi
  • Sakataren gwamnatin Kebbi, Alhaji Yakubu Bala ne ya bayyana hakan lokacin da yake jajantawa waɗanda abin ya shafa
  • Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Dakta Nasir Idris, ta sha alwashin taimakawa duk waɗanda iftila'in ruwan ya shafa

Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alƙawarin taimakawa mutanen da mamakon ruwan sama mai haɗe da iska da aka yi ya yi wa ɓarna.

Vanguard ta ruwaito cewa ruwan ya lalata gidaje sama da guda 100 a garin Zauro, da ke ƙaramar hukumar Birnin Kebbi ta jihar Kebbi.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yauri, shi ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa waɗanda abin ya rutsa da su a garin Zauro.

Kara karanta wannan

Babban Sanata Ya Roki Shugaba Tinubu Ya Sake Buɗe Iyakokin Kasa, Ya Bayyana Dalilinsa

Ruwan sama ya lalata gidaje sama da 100 a Kebbi
Ruwan sama hade da iska mai karfi ya lalata gidaje sama da 100 a jihar Kebbi. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Gwamnatin Kebbi za ta ba da agaji ga waɗanda iftila'in ruwan sama ya faɗamawa

Alhaji Yakubu Bala, ya jajantawa al’ummar Zauro, a madadin gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Dakta Nasir Idris, za ta samar da agajin gaggawa ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.

A cewarsa:

"Ina so in tabbatar muku cewa gwamnati za ta ba da agaji ga waɗanda abin ya shafa."
"Ya kasance al'adar gwamnatin Dakta Nasir Idris, Ƙauran Gwandu a ko yaushe, ba da taimako ga waɗanda suka gamu da wani iftila'i."

Sakataren ya kuma bayyana cewa za su yi zama da hukumomin ba da agaji don duba abinda za su iya yi wa waɗanda abin ya shafa.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman, wanda ɗan asalin garin Zauro ne, Alhaji Shafi’u Zauro ya tattauna da manema labarai kan batun, kamar yadda The Sun ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Babban Lauya Ya Bayyana Mataki Na Gaba da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Bawa da Godwin Emefiele

Shafi'u ya shaidawa manema labaran cewa, gwamna ya umarcesa da ya gaggauta tuntuɓar hukumar ba da agaji ta jihar, SEMA da sauran hukumomin agaji, don tantance gami da ba da taimako ga waɗanda barnar ta shafa.

Hukumar ba da agaji ta ɗauki bayanan waɗanda ɓarnar ruwan saman ta rutsa da su

Shima da yake zantawa da ‘yan jarida a inda lamarin ya faru, babban daraktan hukumar SEMA, Injiniya Abbas Rabi’u Kamba, ya ce hukumar ta ɗauki bayanan waɗanda abin ya shafa da kuma irin ɓarnar da ruwan ya yi musu.

Ya ce an yi hakan ne domin gane irin taimakon da za a yi wa kowane ta ɓangaren kayayyakin abinci da kayan gine-gine.

Alhaji Abbas Kamba ya bayyana cewa sama da gidaje ruwan sama mai haɗe da iskar ya lalata.

Sannan ya kuma shawarci mazauna birane da karkara da su koyi ɗabi'ar dashen itatuwa domin rage tasirin iska.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Jerin Ministocin da Tinubu Zai Naɗa? Gaskiya Ta Bayyana

Dan majalisa mafi ƙarancin shekaru ya bayyana yadda ya shiga siyasa

A wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta batun ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Kebbi da ya fi kowane ƙarancin shekaru a duka 'yan Majalisun Dokoki na Najeriya baki ɗaya.

Ibrahim Bello Mohammed, ɗan majalisa mai wakiltar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza, ya bayyana cewa mutuwar yayansa ce ta sanya shi shiga harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel