Sanata Francis Ya Nemi Shugaba Tinubu Ya Sake Buɗe Iyakokin Kasa, Ya Bayyana Dalilinsa

Sanata Francis Ya Nemi Shugaba Tinubu Ya Sake Buɗe Iyakokin Kasa, Ya Bayyana Dalilinsa

  • Sanata Francis Fadahunsi, wanda ke wakiltar Osun ta Gabas, ya nemi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya buɗe iyakokin Najeriya
  • Sanatan ya ce buɗe iyakokin ƙasar zai taimaka wajen daidaita tattalin arziƙin Najeriya da ya shiga mawuyacin hali
  • Ya kuma yabi Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ya yi na sauya shugabannin tsaro wanda cikinsu har da shugaban hukumar kwastam

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sanata da ke wakiltar Osun ta Gabas a Majalisar Dattawa kuma tsohon mataimakin kwanturola janar na hukumar kwastam, Sanata Francis Fadahunsi, ya bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake bude iyakokin kasar nan da aka rufe domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.

Sanata Fadahunsi ya bayyana hakan ne a wajen wani taron nuna godiya ga Ubangiji bisa sake zaɓensa da aka yi, a cocin St. Paul Anglican da ke Ilase a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa Ya Yi Muhimmin Kira Ga Shugabannin Majalisa, Ya Bayyana Hanya 1 Da Za Su Taimaki Tinubu

An roki Tinubu ya bude boda
Sanata ya nemi Tinubu ya sake bude iyakokin kasa. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Sanatan ya bayyana cewa rufe iyakokin da gwamnatin da ta shuɗe ta yi ya kawo koma baya ga tattalin arziƙin ƙasa, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Sanatan ya ce buɗe iyakokin zai haɓaka tattalin arziƙin ƙasa

Ya jaddada cewa, sake buɗe iyakokin, zai sauya fasalin tattalin arzikin Nijeriya, inda ya ba da tabbatacin cewa, gwamnatin Bola Tinubu na da damar sauya tattalin arziƙin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

“Rufe iyakokin ma wani rashin daidai ne. Mun rufe iyakokinmu ga maƙwabtanmu wanda hakan ya saɓa yarjejeniyar ECOWAS. Tun daga wannan lokacin, mun yi ta fama da matsalar canjin kuɗaɗen waje. Sun lalata mana tattalin arziƙi ta hanyar rufe kan iyakoki.”
“Abubuwa da dama sun taɓarɓare a ƙasar. A yanzu, tattalin arziƙin ƙasa ya yi ƙasa da sifili. Ina yi wa sabuwar gwamnati addu’a ta samu damar farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.”

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Ziyarci Sarkin Musulmi, Ya Nemi Alfarma 1 Tak

Sanatan ya zargi tsohon shugaban kwastam da lalata tattalin arziƙin ƙasa

Ya zargi tsohon shugaban hukumar kwastam da lalata tattalin arziƙin ƙasa bisa irin yadda ya gudanar da ayyukansa.

Ya yabawa Shugaba Tinubu bisa sauyin shugabancin hukumar ta kwastam da ya yi, inda ya bayyana cewa an naɗa wanda ya dace.

Ya bayyana naɗin tsohon shugaban kwastam Hamid Ali a matsayin abinda bai dace ba, tare da ba da tabbacin cewa sabon shugaban yana da ƙwarewar da ake bukata wajen kawo gyara a hukumar.

Buhari ya bayyana cewa da gangan ya rufe iyakokin Najeriya

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan bayanin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na cewa ya rufe iyakokin ƙasar nan ne domin ƙarfafa ma 'yan Najeriya gwiwa su noma wadataccen abinci da za su ci.

Ya ce duk da da farko 'yan Najeriya sun koka kan tsarin, amma daga baya sun yaba da sakamakon da aka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel