Dan Majalisa Mafi Karancin Shekaru Ya Bayyana Yadda Rasuwar Yayansa Ta Sa Aka Tsayar Da Shi Takara

Dan Majalisa Mafi Karancin Shekaru Ya Bayyana Yadda Rasuwar Yayansa Ta Sa Aka Tsayar Da Shi Takara

  • Ibrahim Mohammed, ɗan Majalisar Wakilan da ya fi kowane ƙarancin shekaru ya bayyana yadda ya shiga siyasa
  • Ya bayyana cewa mutuwar yayansa ce ta sanya aka tsayar da shi takara inda daga bisani kuma ya yi nasara
  • Ya kuma sha alwashin yin ingantaccen wakilci ga al'ummar yankinsa ta hanyar shigo da su cikin duk abubuwan da zai riƙa gabatarwa a majalisa

Ibrahim Bello Mohammed, ɗan Majalisar Wakilan da ya fi kowane ƙarancin shekaru a tarihin Najeriya, ya bayyana yadda ya tsinci kansa a matsayin da yake kai a yanzu.

Ibrahim, wanda yake wakiltar mazaɓun Birnin-Kebbi, Kalgo da Bunza, ya kuma bayyana irin tanadin da ya yi wa al'ummar da yake wakilta a hira da ya yi da sashen Hausa na BBC.

Ibrahim Bello Mohammed, dan Majalisar Wakilai mafi karancin shekaru
Dan Majalisar Wakilai mafi karancin shekaru, Ibrahim Mohammed ya bayyana yadda ya tsinci kansa a siyasa. Hoto: Ibrahim Bello Mohammed
Asali: Facebook

Yadda na tsinci kaina a siyasa, ɗan majalisa ya yi bayani

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Nemi Jaruman Kannywood Su Nema Masa Auren Jaruma Zainab Indomie

Ibrahim ya bayyana cewa ya tsinci kansa a hidimar siyasa ne sakamakon rasuwar yayansa, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar PDP a lokacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan rasuwar babban yayansa, marigayi Barista Abba Bello Mohammed, wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP a lokacin, an yanke shawarar tsayar da shi takara inda daga bisani kuma ya ci zaɓe yana da shekaru 27 a duniya, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa:

“Allah ne ya kawo ni cikin siyasa, waɗanda suka sanni, sun san cewa, yayana, uwa ɗaya uba ɗaya, yana takarar wannan kujera, dab kamin zaɓe Allah ya ɗauka ransa.”
“Cikin haka ne al'ummarmu ta ji cikin irin wannan kishi da suke yi mai, za su mara mun, suka jawo ni suka sa na shigo na yi takara kuma ba su bani kunya ba suka zaɓe ni har na kai ga wannan kujerar.”

Kara karanta wannan

Karya suka min: Mai digiri ya fashe da kuka, ya kama kiwon kifi bayan kammala karatu

Ya ce duk da yake yana da ƙarancin shekaru, har yanzu bai taɓa fuskantar wani ƙalubale ba, komai yana tafiya daidai.

Ya kuma ce yana da kyau masu ganin yana da ƙarancin shekaru su sani cewa, shekaru ba su ne ilimi ko basira ba, Allah zai iya ba wanda be kai shi shekaru ba ma.

Ibrahim ya kuma ƙara da cewa lokacin da ya je majalisa ya samu tarba mai kyau daga 'yan majalisu, ba tare da wani ya nuna masa wani bambanci ba.

Ibrahim ya ce zai shigo da mutanen da yake wakilta cikin lamuransa

Ya bayyana cewa zai yi ƙoƙarin bambanta kansa da salon mulkin da wasu 'yan majalisun suke yi ta hanyar komawa cikin mutanen da suka turo shi wakilci domin jin wane saƙo suke da shi.

Sannan ya ƙara da cewa duk abinda zai gabatar, zai yi ƙoƙarin yi wa al'ummar da yake wakilta bayani domin su san abinda yake wakana.

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Ta Ki Bari Su Raya Sunnah

Ya kuma ce babban burinsa a wannan shugabanci shi ne ya ga mutanen da yake wakilta na Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza sun tsayu da kansu wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ya kuma ƙara da cewa zai yi ƙoƙarin ganin ya gina matasa ta fuskar ilimi, kasuwanci da sauran abubuwa na dogaro da kai.

Yadda Ayu da Peter Obi suka janyowa Atiku faduwa zaɓe

Wani labari da Legit.ng ta wallafa, kun karanta batun wani sanata da yake bayani kan yadda Peter Obi da Ayu suka janyowa Atiku faduwa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya ce rigingimun da aka riƙa samu a cikin gida sun taka muhimmiyar rawa wajen faɗuwa zaɓen da Atiku ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel