Zargin Ta’addanci: Tukur Mamu Ya Ɗauki Zafi, Ya Shirya Daukar Mataki Kan Gwamnati

Zargin Ta’addanci: Tukur Mamu Ya Ɗauki Zafi, Ya Shirya Daukar Mataki Kan Gwamnati

  • Tukur Mamu ya yi magana kan zargin daukar nauyin ta'addanci da gwamnatin Najeriya ta ke yi kansa
  • Mamu ya bukaci Ministan Shari'a a Najeriya da ya janye zargin da Gwamnatin Tarayya ke yi kansa ko ya dauki mataki
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin Mamu da wasu mutane kan zargin daukar nauyin ta'addanci a ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tukur Mamu ya bukaci Ministan Shari'a a Najeriya da ya janye zargin da Gwamnatin Tarayya ke yi kansa.

Hakan ya biyo bayan zargin Alhaji Tukur Mamu da kuma wasu mutane kan zargin daukar nauyin ta'addanci a ƙasar.

Tukur Mamu ya dauki mataki kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Tukur Mamu ya bukaci gwamnati ta janye zargin da ta ke yi kansa na daukar nauyin ta'addanci. Hoto: Bola Tinubu, Tukur Mamu.
Asali: Facebook

Wa'adin da Tukur Mamu ya ba gwamnati

Kara karanta wannan

Kano: Daina amfani da soshiyal midiya da wasu sharuɗa da kotu ta kafawa Murja Kunya

Mamu ya rubuta wasika zuwa ga Ministan Shari’a domin tsame sunansa daga cikin wandanda ake zargi da ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da lauyansa ya fitar a ranar 25 ga watan Maris a cewar Tribune.

A cikin wasikar, Mamu ya ba Gwamnatin Tarayya wa'adin kwanaki bakwai domin janye zargin da suke yi kansa.

Ya sha alwashin daukar mataki idan har ba su cire sunansa daga cikin wadanda ake zargi da daukar nauyin taaddanci ba.

“Mu lauyoyin Mista Tukur Mamu wanda muka bayar da umarni da ya shafi daukar nauyin ta’addanci.”
“Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta gurfanarda Mamu a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja.”
"Gwamnatin ta cire sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, kan haka muke bukatar janye wannan zargi cikin kawani bakwai kacal ko kuma mu dauki matakin da ya dace a kotu."

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

- Lauyoyin Tukur Mamu

Bukatar Mamu kan zargin gwamnati

Mamu ya bukaci Ministan Shari'a a Najeriya da ya janye zargin da Gwamnatin Tarayya ke yi kansa

Wasikar ta yi Allah wadai da sanarwar inda ta ce kotu ce kadai ta ke da wannan damar kuma ba ta yi ba, cewar rahoton TheCable

"Yadda mahara ke samun kudin shiga" - Gumi

Kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan yadda aka ayyana wasu tsiraru da daukar nauyin ta'addanci.

Gumi ya ce hakan bai dace ba inda ya ce kotu ce kadai ta ke da ikon ayyana mutum a matsayin mai daukar nauyin ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel