Kungiyar CAN Ta Taya Musulmai Murnar Babban Sallah, Ta Ce ‘Dukkan Mu Yan Uwan Juna Ne’

Kungiyar CAN Ta Taya Musulmai Murnar Babban Sallah, Ta Ce ‘Dukkan Mu Yan Uwan Juna Ne’

  • Kungiyar CAN a Najeria ta taya daukacin 'yan uwanta Musulmai murnar bikin babban sallah da za a yi
  • Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya yi wannan taya murna a ranar Talata 27 ga watan Yuni a Abuja
  • Ya ce dukkan addinan biyu 'yan uwan juna ne, hadin kansu shi zai kawo ci gaban a kasar Najeriya

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta taya Musulman kasar murnar zagayowar bikin sallah babba da za a yi gobe Laraba.

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a ranar Talata 27 ga watan Yuni a Abuja inda ya ce kungiyar na taya daukacin Musulmai murnar bikin sallah.

Kungiyar CAN ta taya Musulmi murnar bikin sallah, ta ce dukkanmu 'yan uwan juna ne.
Shugaban Kungiyar CAN, Rabaran Daniel Okoh. Hoto: PM News.
Asali: Facebook

Okoh ya ce yana fatan wannan bikin sallan zai kawo zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kirista, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

CAN ta bukaci hadin kai tsakanin addinai guda biyu inda ta ce duk 'yan uwan juna ne

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yayin da muke gudanar da wannan babban biki, muna kira ga 'yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya da hadin kai da kuma soyayya a tsakanin juna.
"Mun yi imanin cewa Najeriya za ta cimma burukan da ta saka a gaba idan muka ajiye bambance-bambancen mu a gefe don yin aiki tare saboda gina kasarmu.
"Muna kira ga 'yan uwanmu Musulmai da su yi amfani da wannan bikin sallah don yin addu'ar zaman lafiya da ci gaban kasar mu."

Ya kara da cewa"

"Muna kuma kira ga 'yan Najeriya da su yi addu'a ga shugabannin mu don ubangiji ya ba su hikimar jagorancin kasar."

Kungiyar ta shirya hada kai da Musulmai don samun zaman lafiya

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Shugaban kungiyar har ila yau, ya jaddada himmatuwar kungiyar don ganin an samu zaman lafiya a tsakanin addinai da kuma 'yan Najeriya baki daya, Daily Trust ta tattaro.

Ya ce:

"Mun yi imanin cewa Najeriya za ta samu ci gaba idan muka yi aiki tare da kuma mutunta addinan juna.
"Muna addu'an Ubangiji ya kara albarka ga kasar da kuma ba mu zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaba."

Sallah: Kiristoci Sun Taya Musulmai Sharar Filin Idi A Kaduna

A wani labarin, Kiristoci a Jihar Kaduna sun taya Musulmai sharar filin Idi a garin Kachia don shirin bikin sallah.

Kiristocin sun taya Musulman sare ciyayi don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin addinan guda biyu.

An tattabar cewa Kiristoci maza da mata ne suka halarci wannan aikin gayya a filin Idin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel